Za a rika yi wa masu fyade daurin rai da rai
Majalisar Dattawa ta amince da dokar laifuffukan jima’ai ta shekarar 2015, wadda ta tanadi daurin rai da rai ga masu fyade da kuma wadanda suka yi lalata da kananan yara mata ’yan kasa da shekara 11. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ya ce shekaranjiya Laraba ne majalisar […]
Majalisar Dattawa ta amince da dokar laifuffukan jima’ai ta shekarar 2015, wadda ta tanadi daurin rai da rai ga masu fyade da kuma wadanda suka yi lalata da kananan yara mata ’yan kasa da shekara 11.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ya ce shekaranjiya Laraba ne majalisar ta amince da dokar bayan karbar rahoton Kwamitin Shari’a da Kare Hakki dan Adam da Harkokin Shari’a da Sanata Umaru dahiru na APC daga Sakkwato ya shugabanta.
Da yake mika rahoton Sanata Umaru dahiru ya ce amincewa da dokar zai samar da dokar da za a rika hukunta masu aikata ayyukan lalata da mata da karfi.
Ya ce idan aka amince da kudirin masu fyade ga kananan yara za su karasa rayuwarsu a kurkuku, yayin da masu aikata sauran ayyukan lalata za su sha dauri iri-iri don zama darasi ga sauran jama’a.
Shugaban Majalisar Dattawan mai barin gado Sanata Dabid Mark ya nuna farin cikinsa kan kokarin kwamitin na samar da doka mai karfi ga masu aikata fyade, “Ina mika godiya da taya murna ga wadda ta gabatar da wannan kudiri Sanata Chris Anyanwu,” inji Mark.
Da take ganawa da manema labarai bayan tashi daga zaman majalisar Sanata Anyanwu ta APGA daga Jihar Imo, ta ce amincewa da dokar tamkar kyautar ban-kwana ta yi wa jama’ar kasa.
“Hakika wannan wani cika buri ne na Majalsar Dattawa,” inji ta.
Ta lissafo abubuwan da dokar ta kunsa da suka hada da mutane da yawa su hadu su yi fyade, ko sanya abu mai bugarwa don a yi fyade ko harbar abokin jima’i da cutar kanjamau ko wata cuta da sani.
Ta ce sauran sun hada da kai yara mata kasashen waje don karuwanci da musgunawa ta hanyar jima’i da sanya masu tabin hankali a karuwanci ko lalata da masu tabin hankali.
Sanata Anyawu ta ce kudirin dokar ya bukaci a adana sunayen wadanda suka aikata fyade don daukar mataki a kansu a gaba. “Wadanda aka samu da laifi ba za a taba ba su aiki a kowace hukuma ko ma’aikata ta gwamnati ba, domin kada su zamo barazana ga sauran jama’a. Kun ga hakan hukunci ne mai zafi,” inji ta.
Kuma ta ce duka wanda aka samu da laifi za a tilasta shi yin gwajin lafiya, yayin da “wadanda suka yi karyar wani ya yi musu fyade, su ma za a hukunta su idan suka kasa gabatar da shaida,” inji ta.