Za a rufe filin jirgin saman Legas daga ranar 1 ga watan Oktoba

Za a rufe shi ne domin yi wasu gyare-gyare

Za a rufe filin jirgin saman Legas daga ranar 1 ga watan Oktoba

Filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Legas

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayar da umarnin rufe sashen saukar jirage na kasa da kasa a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Za a fara rufewar ce daga ranar 1 ga watan Oktoban 2023.

Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin wata ziyararsa a filin jirgin na Legas ya ce za a rufe filin ne domin a samu damar yin wasu gyare-gyare a cikin shi.

Yayin rangadin, ya sami rakiyar Shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Kabir Yusuf Mohammed.

Hakan na zuwa ne bayan Ministan ya sanar sa soke jinginar da filayen jiragen saman na Legas da na Malam Aminu Kano da ke Kano, wanda gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Ya kuma dakatar da ci gaba da aikin kafa kamfanin jiragen sama mallakin Najeriya na Nigeria Air,har sai abin da hali ya yi.

Aminiya ta rawaito yadda gwamnatin da ta gabata ta cefanar da filayen jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Malam Aminu Kano da ke Kano.

To sai dai lokacin da yake zagaya filin jirgin saman Legas a ranar Alhamis, Festus Keyamo, a ziyararsa ta farko tun bayan zama Minista, ya ce an dakatar da cefanar da filayen da kuma shirin fara Nigeria Air har sai nan gaba.

Ayyukan guda biyu dai sun matukar janyo ce-ce-ku-ce saboda an aiwatar da su ne ’yan kwanaki kafin cikar wa’adin Buhari.

Ya kuma ce kamfanin CAAC na Amurka, wanda ya kunshi kungiyar filayen jiragen sama ta Amurka da kamfanin Mota Engil Africa da Mota Engil Nigeria ne suka samu damar jinginar flayen.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa