Za a rufe karbar labaran Gasar Hikiyata ranar Lahadi 22 ga Agusta

Labarin “Sansanin Gudun Hijira” ne ya lashe gasar ta farko,

Za a rufe karbar labaran Gasar Hikiyata ranar Lahadi 22 ga Agusta

Maryam Umar da ta lashe gasar ta bara Hoto: BBC Hausa

A ranar Lahadi 22 ga Agusta ce za a rufe karbar labaran shiga Gasar Hikayat ta BBC Hausa ta bana.

Ita dai gasar Hikayata an kirkire ta ce a 2016 domin karfafawa mata gwiwar cigaba da rubuce-rubuce domin su ba da labarinsu da kansu.

Ana shiga gasar ce da kagaggen labari wanda mace ta rubuta kuma ya kasance mai yawan kalma 1000 zuwa 1500.

Sannan alkalai ne za su zauna domin tantancewa tare da fitar gwarazan gasar guda uku, da kuma wasu wadanda suka cancanci yabo

Da yake magana kan gasar, Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko ya ce, “mun samu nasara matuka a shekara shida da muka yi muna shirya wannan gasar.

“Gasar Hikiyata ta ba mata da dama damar bayyana labarinsu.

“A bara mun samu labarai 400 da suka shiga gasar a duk fadin duniya, kuma ina tunanin na bana zai fi haka yawa.”

A nasa bangaren, Shugaban Sashen Yarukan Afirka ta Yamma na BBC, Oluwatoyosi Ogunseye ya ce, “ina farin cikin ganin cewa bana ma muna shirin Hikayata.

“Mata suna cikin tsarin BBC kuma za mu cigaba da ba gasar gudunmuwar da ta dace.

“Muna matukar ganin muhimmancin Hausawa masu saurarenmu saboda yadda suke kasancewa tare da mu.”

Maryam Umar, mai shekara 20 ’yar asalin Jihar Sakkwato da take karantu a sashen nazarin shari’a ce ta lashe gasar ta bara da labarinta mai suna “Rai da Cuta”.

Labarin “Rai da Cuta” ya kunshi wata mai suna Azima, wadda mijinta ya dawo daga tafiya yana nuna alamun cutar Coronavirus, kuma duk da tana dauke da juna biyu, sai ya ki killace kansa, domin bai yarda da cutar ba.

Hakan ya sa Azima ta kulle shi a daki, amma daga baya ta gane ta riga ta kamu da cutar, wadda ta sa ta rasa juna biyunta, sannan ta sha fama da ciwo mai tsanani.

A cewar Maryam, “Hikayata ta bude min damammaki da yawa a rayuwa wadanda ban ma yi tsammanin zai kai gare su ba.

“Gasar ta zama hanyar daukakata, na zama fitacciya sannan na zama miloniya.

“Gasar kamar hakar gwal ce, na hazo tawa. Ina fata mata za su feke alkalumansu.”

Labarin “Sansanin Gudun Hijira” ne ya lashe gasar ta farko, wanda ya bayyana halin da ’yan gudun hijira suke ciki.

Za a iya tura labarai domin shiga gasar zuwa [email protected] zuwa ranar 22 ga Agusta.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja