Za a rufe kasuwar canji ta Abuja ranar Alhamis

Darajar Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin Najeriya.

Za a rufe kasuwar canji ta Abuja ranar Alhamis

’Yan kasuwar canji da ke Abuja sun sanar da rufe kasuwa daga gobe Alhamis har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ake fama da ita a kasar.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar canjin, Alhaji Abdullahi Dauran ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Darajar Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin Najeriya.

A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.

Kungiyar ’yan canji ta alakanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kudade ta Intanet irin na Crypto da ake kira Binance.

Hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta hana ’yan Najeriya hulda da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.