Za a rufe makarantun kiwon lafiya da asibitocin kudi a Kaduna
Gwamnatin ta ce dole duk mai son bude asibiti ko kwaleji ya fara yin rajista kafin komai.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana kudurinta na rufe dukkanin kwalejojin kiwon lafiya da asibitocin kudi da ba su da rajista a jihar.
Kwamishinar Lafiyar Jihar Kaduna, Dokta Amina Baloni, ta ce ma’aikatarta ta riga ta fara bincike don gano makarantun koyon aikin kiwon lafiya marasa rajista a jihar.
- Najeriya A Yau: ’Yan Siyasa Na Buya Saboda IPOB A Anambra
- Za a fara biyan daliban jami’a alawus din N75,000
Ta ce a yanzu akwai sama da asibitoci 1,000 masu rajista da ma’aikatar lafiya ta jihar, amma duk da haka akwai wasu da dama marasa rajista.
Dokta Baloni ta ce akwai sharuda da ya kamata a bi kafin bude makarantun kiwon lafiya, wadanda ta ce matukar ba a cika su ba to za a rufe makarantar da aka kama.
“Ba za ka bude makaranta ba tare da ka yi rajista ba, daga bisani ka zo ka ce kana son yin rajista; Ko kasuwanci bai kamata ka fara ba tare da ka yi rajista ba, ballantana harkar kiwon lafiya, don haka muna nan zuwa kan wadannan mutane.
“Wadanda suke da rajista kuma za a neme su don su zo a tabbatar musu da rajistarsu.
“Don kawai mutum yana da lasisin zama likita shi ke nan sai ya je ya bude kwaleji ko kuma asibiti, hakan ya saba da doka,” a cewarta.
Kazalika, ta shawarci iyaye da su guji tura ’ya’yansu makarantun kiwon lafiya na kudi don mallakar shaidar karatu ta bogi.