Za a rushe gidan da aka boye yaron da aka yi garkuwa da shi a Abekuta

Rundunar ’yan sanda za ta rushe gidan da aka boye yaron nan dan shekara 4 da aka yi garkuwa da shi a Abekuta.Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun Abdulmajeed Ali ne ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargi da yin garkuwa da yaron a harabar babban ofishin ’yan sanda da […]

Za a rushe gidan da aka boye yaron da aka yi garkuwa da shi a Abekuta
Za a rushe gidan da aka boye yaron da aka yi garkuwa da shi a Abekuta

Rundunar ’yan sanda za ta rushe gidan da aka boye yaron nan dan shekara 4 da aka yi garkuwa da shi a Abekuta.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun Abdulmajeed Ali ne ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargi da yin garkuwa da yaron a harabar babban ofishin ’yan sanda da ke a Eleweron, Abekuta.
Tun da farko dai sai da masu garkuwar suka fara boye yaron a wani gida a Abekuta har na tsawon kwanaki 8, sannan daga bisani suka garzaya da shi wani kauye a garin Nsukka a Jihar Enugu domin, ’yan sandan da suka kubutar da yaron sai da suka yi tafiyar awa 9 a baburan da suka dau haya daga garin Nssuka, a inda suka kubutar da yaron suka kuma kame wadanda suka yi garkuwa da shi.
A cewar kwamishinan, muddin mai gidan da aka yi garkuwa da yaron bai kai kansa ofishin ’yan sanda ba nan ba da jimawa ba, to rundunar ’yan sandan Ogun za ta yi hadin guiwa da ta Enugu, su rushe gidan bisa tanadin da doka ta yi.
Ya shaida cewa nasarar da suka samu na kubutar da yaron da ma kame wadanda ake zargi ta ta’allaka ne bisa cikekken goyon baya da iyayen yaron suka ba ’yan sandan, da ma uwa-uba Naira miliyan dayan da iyayen yaron suka ba masu garkuwar, wanda daya daga cikinsu ya karba a wani wuri a Abekuta.
Wadanda ake zargin sune Kenechukwu Amoke dan shekara 21, Anayo Amoke dan shekara 35 da Oluchi Asadu mai shekaru 20, sai Maureen Uchenna ’yar shekara 25, wacce a da take aikin jinya a asibitin da iyayen yaron kan je a duba lafiyarsu. Ita ce ta tsaegunta wa saurayinta Anayo, cewa iyayen yaron masu wadata ne; wanda hakan ya sanya saurayin nata yin garkuwa da shi domin karbar kudin fansa.
Mahaifin yaron, Municipal Kanu ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu yaron ya dawo cikin danginsa, za kuma a kai shi asibiti a duba lafiyarsa saboda irin ramar da ya yi.  Ya kuma mika godiyarsa ga dinbin mutanen da suka taya su alhini, a lokacin garkuwar da jami’an ’yan sandan da suka kubutar da shi da ma ’yan jaridar da suka yi ta yayata labarin.