Za a rushe sassan gidan sarki ne don gyare-gyare – Masarautar Kano

Masarautar Kano ta bayyana cewa za ta rushe wasu wurare a gidan sarki ne don gudanar da wasu gyare-gyare a masarautar, ba wai don gina ofisoshin hakimai ba. Wannan bayani ya fito daga bakin mai magana da yawun masarautar, wanda kuma shi ne danmajen Kano, Alhaji Munir Sanusi, a lokacin da yake mayar da martani […]

Za a rushe sassan gidan sarki ne don gyare-gyare – Masarautar Kano
Za a rushe sassan gidan sarki ne don gyare-gyare – Masarautar Kano

Masarautar Kano ta bayyana cewa za ta rushe wasu wurare a gidan sarki ne don gudanar da wasu gyare-gyare a masarautar, ba wai don gina ofisoshin hakimai ba.

Wannan bayani ya fito daga bakin mai magana da yawun masarautar, wanda kuma shi ne danmajen Kano, Alhaji Munir Sanusi, a lokacin da yake mayar da martani ga karar da wani Alhaji Salim Abubakar Bayero ya shigar gaban wata babbar kotun jiha; inda yake kalubalantar mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhamamdu Sanusi II da Masarautar Kano game da rushe wani yanki na masarauntar Kano da yake shirin yi.
A takardar karar da ya shigar, Alhaji Salim, wanda kawu ne ga Sarkin Kano, kasancewarsa daya daga jikokin Sarkin Kano Abdullahi Bayero; ya bayyana cewa yana neman kotu da ta tsayar da sarkin daga gudanar da rushe-rushe a wasu wurare da suka hada da Ka’iya da Kachako da kuma wasu kaburbura da ke cikin gidan sarkin mai dadadden tarihi (Gidan Rumfa) da nufin gina ofisoshi ga hakimai. A cewar takardar karar, tuni masarautar Kano ta raba takardar sanarwa ga wadanda wannan aikin zai shafa, da su tattara kayansu su bar wuraren kafin lokacin gudanar da wancan rushe-rushe.
Bayan sauraren karar, mai shari’a A.T. Badamasi ya dage shari’ar zuwa ranar 12 ga wannan wata.
Alhaji Munir Sanusi ya bayyana cewa gidan Sarki ba gidan adana kayan tarihi ba ne, ballantana a ce ba za a yi masa kwaskwarima ba. “Ya kamata jama’a su fahimci cewa gidan sarki ba gidan adana kayan tarihi ba ne, wanda za a ce za a bar shi saboda ’yan baya. Idan an duba a da can, duk bukkoki ne a gidan amma a yanzu ya canza. Wannan ya nuna cewa ba a yanzu aka fara yi wa wannan gida kwaskwarima da gyare-gyare don ya dace da zamani ba. Dukkanin sarakunan da suka zauna a gidan sun gudanar da gyare-gyare a wannan gida. Idan an duba masarautar Sakkwato, a kwanan nan ma gaba daya aka rushe ta aka sake gina ta. Don haka wanann ba sabon abu ne da zai zama abin Magana.” Inji shi.
danmaje ya bayyana cewa rushe wasu wuraren na gidan sarkin ya zama dole, idan an yi la’akari da yadda kasa ke fadowa a kan mutane tana jawo musu raunika. “A wasu lokutan daukar matakin rushe wasu wuraren abu ne da ya zama dole, domin idan aka bari kasa ce za ta fado ta danne mutane, wanda Allah ne kadai ya san asarar da hakan za ta haifar ta rai da kuma ta dukiya. Ko a kwanakin baya irin wannan ginin ya fado a kan wani mutum, wanda har ya sami raunika sakamkon hakan. To ba ma fatan irin hakan ta sake faruwa.” Inji shi.
Har ila yau, danmajen na Kano ya yi yi kira ga jama’a da su ba masarautar Kano hadin kai wajen zama da junansu lafiya. A cewarsa, gidan sarki na kowa ne, don haka Sarki ba shi da niyyar korar kowa daga gidan. “Muna so duk jama’a su zauna lafiya da junansu tare da kwantar da hankulansu. Jama’a su sani cewa gidan nan na kowa ne, ba na sarki ba ne, haka kuma mai martaba ba shi da niyyar korar kowa daga wannan gida. Kowa ya kwantar da hankalinsa.” Inji shi.
Dangane da karar da aka shigar kuwa, wata majiya mai karfi ta tabbatar wa Aminiya cewa mai karar ya mika takardar bukatar janye kararsa daga kotun Mai shari’a A. T. Badamasi.