Za a saki fursunonin Taliban duk da kin amincewar Amurka

Gwamnatin Afghanistan na shirin sakin fursunoni 37 na ’yan kungiyar Taliban da ke tsare a kurklukun Bagram, duk da kin amincewar kasar Amurka. Tun a a ranar tara ga Janairun bana gwamnatin kasar a birnin Kabul ta ba da sanarwar shirinta na sakin fursunoni 72 da ake tsare da su, saboda ba a samu hujjojin […]

Za a saki fursunonin Taliban duk da kin amincewar Amurka

Kurkukun Gab ram da ke kasar AfghanistanGwamnatin Afghanistan na shirin sakin fursunoni 37 na ’yan kungiyar Taliban da ke tsare a kurklukun Bagram, duk da kin amincewar kasar Amurka. Tun a a ranar tara ga Janairun bana gwamnatin kasar a birnin Kabul ta ba da sanarwar shirinta na sakin fursunoni 72 da ake tsare da su, saboda ba a samu hujjojin da ke nuni da laifukan da ake tuhumarsu ba, kamar yadda wani jami’in hukuma ya bayyana.
Rundunar sojan Amurka da Afghanistan ta soki lamirin labarin sakin fursunonin, inda ta bayyana cewa “’’yan kunar bakin wake ne masu hadari,” wadanda “hannunsu ya yi nashe-nashe da jinanen al’ummar Afghanistan.”
“Hukumar bin kadi ta ARB za ta sako ’yan kunar bakin wake masu hadari a cikin al’umma, wadanda hannayensu ke jike da jinin ’yan Afghanistan,” a cewar rundunar sojan Amurka da ke Afghanistan.