Za a saki mutum 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da Boko Haram a Borno

Mutanen da za a saki ba su da wata mummunar aƙida mai barazana da kasancewarsu a cikin al’umma.

Za a saki mutum 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da Boko Haram a Borno

Rundunar Sojin Najeriya za ta saki wasu fursunoni fiye 200 waɗanda aka wanke daga zargin alaƙa da kungiyar Boko Haram a Maiduguri.

Rundunar sojin dai ta kama mutanen ne a lokacin da ta’addancin Boko Haram ya tsananta a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Binciken wakilinmu ya gano cewa rundunar za ta miƙa waɗannan mutane ne ga gwamnatin Jihar Borno domin dawo da su cikin al’umma.

Bayanai sun ce za a miƙa wa gwamnatin mutanen ne a ranar Talata a barikin Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Majiyarmu ta bayyana cewa, Kwamishinar Mata ta Jihar Borno, Zuwaira Gambo da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Farfesa Tar Umar ne za su karɓi mutanen da aka wanke daga zargin alaƙa da ƙungiyar ta’addan.

Sojojin sun bayyana cewa a iya binciken da aka gudanar an gano cewa ba su da wata mummunar aƙida mai barazana da kasancewarsu a cikin al’umma.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS