Za a samu canji a Kaduna idan na zama Gwamna – El-Rufa’i
Malam Nasir el-Rufai dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna ne a karkashin jam’iyyar APC. A wata hira da wakilinmu kwanakin baya, bayan bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fidda gwani. Ga yadda hirar ta kasance. Aminiya: Lokacin da kake Ministan Babban birnin Tarayya Abuja wasu na maka kallon wani mutum wuyar sha’ani […]
Malam Nasir el-Rufai dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna ne a karkashin jam’iyyar APC. A wata hira da wakilinmu kwanakin baya, bayan bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fidda gwani. Ga yadda hirar ta kasance.
Aminiya: Lokacin da kake Ministan Babban birnin Tarayya Abuja wasu na maka kallon wani mutum wuyar sha’ani musamman lokacin shirinka na canza fasalin birnin ta hanyar gudanar rusau. Shin za ka maimaita hakan a Kaduna idan aka zama gwamna?
El-Rufa’i: Ban fahimci abin da kake nufi da kalmar wuyar sha’ani ko tsatsaurar ra’ayi ba. Na sha fadawa jama’a cewa ba ni da wuyar sha’ani. Ka dube ni da kyau ni ba mutum ba ne mai girman jiki sannan ni ba karfarfa ba ne. Kafin shekarar 1999 lokacin da na zama shugaban Hukumar Sayar da Kamfanonin Gwamnati (BPE) babu wanda ya sanni. Da ina da wuyar sha’ani da an sanni. Ina ganin rashin sa’a ko kuma in ce sa’ar da nake yi shi ke ba ni aiki masu wuya da wasu ke tsoron yi da ake yi ya sa wasu ke dauka na ina da wuyar sha’ani. Aikina a BPE shi ne sayar da kaddarorin gwamnati abu ne mai wuyar sha’ani. Ba el-Rufa’i ke da wuyan sha’ani ba, aikin ne.
Domin jama’a sun saba gwamnati ke yi masu komai tafiyar da wayannan abubuwa na da wuyar sha’ani kuma a kasar nan idan ka ce za ka yi aiki yadda ya kamata ko yake a rubuce, to za ka sha kalamai marasa dadde, ciki har da ce maka kana da wuyar sha’ani. Ni ba ni da matsala domin aiki na kawai nake yi. Lokacin da nake mai bai wa tsohon Shugaban kasa Abdulsalami Abubakar shawara, ai babu wanda ya sanni tun da aiki na kawai shi ne ba da shawara. Ni idan aka ba ni aiki har na yarda zan yi aikin to ina yinsa ne da zuciya daya.Matsayina a lokacin na Ministan Babban birnin Tarayya Abuja wanda aiki ne mai matukar wahala. Na yi aikin ne da zuciya daya. Kuma a wannan lokacin zan ce shi ne ba maganar ina da wuyar sha’ani ba ne ko a’a. Abin tambaya shi ne ko na bar Abuja fiye da yadda na tarar da ita. Ina kuma ganin mazauna garin za su tabbatar maka da cewa eh, kuma ina ganin abin da ya da ce a yi ke nan.
Zancan Kaduna kuwa, ina ganin Jihar Kaduna na da bambanci da Abuja ta hanyoyi daban-daban. Akwai ayyuka da ya kamata mu yi a nan. Ba kuma duka ayyukan da za mu yi anan ba ne jama’a za su so. Amma da yawan jama’a za su ji dadinsu. Idan har jama’a suka zabe mu ke nan suna neman canji. Ke nan ba su san jihar ta zama wajen kafa manyan fastoci amma babu aikin komai. Ke nan suna bukatar makarantu su inganta fiye da yadda suke a yanzu, ke nan suna bukatar asibitocinmu su inganta yadda kowa zai amfana ba sai wanda ke da kusanci da gwamnati ba za’a dauki nauyinsa zuwa kasar Masar neman magani. Za a samu canji a Jihar Kaduna idan na zama gwamna. Kuma ana bukatar harkokin noma su bunkasa haka kuma ana bukatar kawo karshen kashe-kashe a jihar baki daya. A yanzu haka wadannan abubuwa babu su a jihar. Idan kuma muka ce zamu yi sai wasu su ce wai muna da wuyan sha’ani. Bari in baka misali, a yankin Birnin Gwari ana yawan satar shanun mutane da kuma fashi da makami, an kuma kasa kawo karshen matsalar. Me ya sa haka idan ba rashin mayar da hankali akai ba. Mun fito da manufofinmu da shirye-shiryenmu ga alummar Jihar Kaduna domin inganta rayuwansu. Kuma zamu yi hakan da zarar mun samu damar hakan.Abin da mutanen Kaduna ke so ke nan. Kuma za mu yi masu su insha Allah. Duk abin da zamu yi sai mun tattauna da jama’a kamar yadda tsarin dimukradiyya ya shinfida.
Aminiya: Akwai lokacin da ka je gidan rediyo kana bayanin ingantattcen zabe, amma kana daya daga cikin ’yan PDP a shekarar 2003 wadanda aka zarga da hannu wajen magudin zabe a wancan lokaci. Me za ka ce?
El- Rufa’I: Kuskure ne ka kwatanta jam’iyyar PDP a shekarar 2003 da PDP ta Jonathana yanzu. PDP da nake a ciki ta bambanta da ta yanzu. Bari na ba ka misali, a lokacin ina Ministan Abuja na rusa gidan shugaban jam’iyyar PDP, a yau babu ministan da ya isa ya rusa gidan wani jigo a jam’iyyar PDP. Saboda haka akwai bambanci PDP da, da ta yanzu. ’Yan PDP na 1999 sun bambanta matuka da na yanzu. ’Yan PDP yau, marasa gaskiya ne.
Ba sa mutunta doka. Sun ce jam’iyyarsu ta mutane ce amma ba su mutunta mutanen sannan ba su mutunta dimukradiyya. Idan kana da ja sai ka je ka duba yadda suka gudanar da zaben fidda gwaninsu na kwanan nan. Saboda haka, ka daina kwatanta PDP wacen lokaci da ta yanzu. Na kasance minista a gwamnatin PDP, amma ba an sanya ni minista ba ne saboda ni dan PDP ne. A’a cancanta aka duba aka nada ni minista.
Ba kuma wakiltar wat jiha nake ba a lokacin, domin ministar da ke wakiltar Kaduna ita ce Nenadi Usman. Saboda a lokacin gwamnan da ke jihar ya kini a lokacin saboda wai ban taimakawa jam’iyar ba. Shi kuma Shugaba Obasanjo ya fada masa cewa dole sai na yi minista saboda akwai aikin da yake so na yi masa. Duk da cewa ina minista a jam’iyyar PDP ra’ayinmu ya bambanta da su. An shigo da mu gwamnati ne ba domin muna ’yan PDP ba, amma sai saboda cancantarmu. Misali ni Dokta Ngozi Okonjo-Iweala da Obi Ezekwesili da sauranmu.
Ana yi mana lakabi da masu tsautsaurar ra’ayi, a matsayina na minista ina rike ne da mukamai biyu a jam’iyyar PDP.
A matsayina na dan Jihar Kaduna ina cikin wakilan PDP na kasa, amma sai ka je ka duba ko na taba halartar taronta ko da sau guda. A lokacin ina ganin bata lokaci ce siyasa. Har ila yau, a matsayina na minista ni ne shugaban PDP a Abuja, amma sai ka je ka duba waye ya ci zabe a shekarar 2007, dan jam’iyyar ANPP ne ya ci. Wannan ya faru ne saboda na gargadi duk shugabannin jam’iyyar cewa duk wanda ya yi magudin zabe. To sai na sa EFCC a lokacin Malam Nuhu Ribadu ta kamashi. Amma abin bakin ciki sai ga Nuhu Ribadu ya koma PDP.
Babu ruwana da wa ya ci zaben ni dai kawai abin da nake so shi ne a yi zabe mai inganci. Ban taba magudin zabe ba saboda idan na yi ba zan iya barci ba. Saboda haka ban taba yi ba.
Aminiya: A zamanin kana minista ka rusa sakatariyar ’yan jarida da ke Abuja, ke nan idan aka zabeka Gwamnan Jihar Kaduna za ka sake maimaita hakan?
El-Rufa’i: kungiyar ’yan jarida na lokacin suna zaune ne a wani guri na wuncin gadi a Abuja. Bari in baka dan gajeran tarihi akan abin da ya sa har muka yi abin da mu ka yi. A lokacin da aka mayar da cibiyar gwamnati zuwa Abuja a shekarar 1991. An bukaci ’yan jarida su dawo Abuja, amma kuma ga shi ba su da wajen zama. Daga nan sai aka ba su wata makarantar firemare su yi amfani da ita na wani lokaci a unguwar Garki. Wajen na makarantar firamare ne domin a lokacin babu dalibai.
Daga bisani an bai wa kungiyar ’yan jaridan wani fili domin su gina sakatariyarsu, amma sai ba su yi hakan ba. Kai har wani tallafi na kudi aka ba su domin su gina wajen. Kana iya zuwa ka tambaye wadanda suka amsa kudin abin da suka yi da shi. Lokacin da muka shigo ofis sai na duba takardu, inda na ga cewa ministan da ke a ofis kafin ni ya yi wa ’yan jaridan alkawarin miliyan uku domin karasa wannan gini, amma kudin bai kai hannunsu ba. Ina shiga na amince a biya wadannan kudi domin su samu damar karasa ginin sakatariyarsu. Da muka zo muna binciken yawan makarantun firamaren da muke da su a Abuja, sai muka gano cewa ai inda ’yan jarida suke amfani da shi makarantar firamare ce, kuma sai gashi muna da karancin makarantu saboda cinkosan mutane a yankin Garki.
Daga nan sai muka duba wane ne yafi mahimmanci tsakanin yaranmu dalibai da kuma sakatariyar ’yan jarida. Ni dai kam na fi daukar yaranmu da mahimmanci domin haka sai na aika aka kirawomin Shugaban ’yan jarida na kasa, Smart Adeyemi. Na fada masa cewa gwamnati ta baku fili da kudi da zaku gina wajen, amma wasu sun karkatar da kudin. Ministan da ke bi mini ya yi muku alkawarin miliyan uku amma bai cika ba sai da nazo na biya.
Saboda haka na ba ku watanni shida ku tashi daga wajen tun da dama na wuncin gadi ne. Ina kuma san in mai do da ’yan makaranta wajen tun da dama makaranta ce. Sai ya ce ai zai yi wuya su kammala gininsu a wata shida ni kuma sai na ce masa ya je ya nemo wani ofis zan biya masu kudin haya na shekara biyu. Amma sai ya dauka ko saboda ’yan jarida ne su ba zan iya taba su ba.
Baya ga haka kuma an gina otel a cikin sakatariyar, inda suke shalholiyarsu da daddare. Daga baya dai mun rusa wajen muka mayar da shi domin mayar da shi makaranta. Tun kuma daga lokacin ne Smart Adeyemi wanda sanata ne a yanzu ya mayar da ni makiyinsa. Amma ni ban damu ba kuma ban yi da na sanin abin da na yi ba tun da dai jama’a ake wa aiki. Kuma wajen nan dama ba wai na ’yan jarida ba ne. An bayar ne kawai na wuncin gadi.