Za a samu karancin masara a 2021 —Manoma
Manoma sun bayyana abin da zai kawo karancin masara a Najeriya
Manoma sun yi hasashen cewa za a samu karancin masara a shekarar 2021 mai kamawa a Najeriya.
Kungiyar Manoma Mazauna na Oke-Ogun sun dora laifin kan raunin hasashen yanayin da aka yi da kuma gazawar gwamnati wurin samar da kayan noma.
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
- ’Yar Shaikh Ibrahim Nyass ta rasu
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 48, sun kashe 2 a Katsina
A jawabin kungiyar manoman na yankin Oke-Ogun na Jihar Oyo da ke zaman tushen abinci a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, ’ya’yanta sun yi asarar miliyoyin Naira a daminar 2020 sakamakon ‘gazawar gwamnati wurin taimaka wa amfanin gona.’
A taron gaggawarta domin share hawayen manoman masara a Jihar Oyo, kugiyar ta ce manoma da dama sun zabi su daina noman masara nan gaba saboda rashin samun kayan noma.
Shugabanta, Alabi Kazeem ya ce daga baya, hasshen samun ruwa a watan Oktoba da Nuwamban 2020 ya sa suka gaggauta ci bashi don su noma masara da tunanin za su ci riba, amma aka samu akasi, suka tafka mummunar asara.
Don haka ya roki gwamnati ta tallafa musu domin su samu biyan basukan da suka ci domin noma masarar da suka yi asara.
Sun shawarci gwamnatocin jihar da ta Tarayya da Babban Bankin Najeriya su dauki matakan kawar da karancin abinci musamman masara a 2021, duba da muhimmancinta ga al’umar Najeriya.
Taron ya roki Shugaba Buhari ya rika amfani da hasashen yanayi wurin tsara tallafin da ya dace ga manoma na ainihi.
Sun roki gwamnan jihar ya cika alkawarinsa na sanya su a masu cin gajiyar rancen da jihar ta samu na farfado da al’ummomin manoma, kasancewar kungiyar na wakiltar kananan hukumomi 10 a jihar.
“Tsoronmu shi ne talakawa da za su shiga mawuyacin hali sakamakon karancin muhimman kayan abinci kamar masara,”inji kungiyar.