Za a samu sauyi mai ma’ana a 2015 – Alhaji Tukur
Alhaji Muhammad Tukur wani dan siyasa ne da ke JIhar Kuros Riba wanda kuma ya tattauna da Aminiya a kwanakin baya, inda ya bayyana cewa ko shakka babu matukar ’yan Najeriya musamman matasa suka jajirce suka ki bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen bangar siyasa, to lalle kasar nan za ta samu […]
Alhaji Muhammad Tukur wani dan siyasa ne da ke JIhar Kuros Riba wanda kuma ya tattauna da Aminiya a kwanakin baya, inda ya bayyana cewa ko shakka babu matukar ’yan Najeriya musamman matasa suka jajirce suka ki bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen bangar siyasa, to lalle kasar nan za ta samu sauyin da take bukata. Ga yadda hirar ta kasance.
Aminiya: Yaya kake ganin asakala tsakanin jam’iyyar PDP da kuma ta adawa wato APC?
Alhaji Tukur: Idan ’yan jam’iyyar APC suka hada karfi da karfe suka fitar da son zuciya da kyasin juna a siyasance, tabbas za su iya karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP. Saboda na lura a kasar nan jama’a da daman gaske sun gaji da mulkin PDP tun daga matakin kasa har zuwa sama. Idan suka yi siyasar lumana ba wai, ba nuna bangaranci ko cusa ra’ayi na sukar addini. To za mu samu sauyi mai ma’ana a 2015.Yawancin jama’a sun san mafitar guda daya ce shi ne a tsaya kan gaskiya, idan an tsaya a kan gaskiyar nan in sha Allahu muna ganin za a samu ci gaba da kuma sauyi. Domin a ceto kasar daga cikin halin da ta tsinci kanta domin kowa yasan halin da kasar take ciki ba shi da dadi.
Aminiya: Ta yaya kake ganin zabe zai gudana lura da cewa a wasu jihohin duka manyan jam’iyyun suna fama da rikicin cikin gida?
Alhaji Tukur: Idan ’yan siyasa suka kawar da akidar idan dai ba ni ba, to kowa ya rasa. Amma akwai sarkakiya a cikin lamarin idan har a ce kai ka fito wannan ma ya fito, kuma wani bai hakura ya barawa mini. Hada za su yi domin su yaki wancan bangaren. Hakan ne kawai zai kawo musu nasara su yi yaki a siyasance, ba ina nufin yaki da makami aika ’yan bangar siyasa su afkawa abokan adawa.
Aminiya: Yaya kake kallon barazanar da ’yan yankin Neja-Delta suke yi cewa ba za su yarda dan yankinsu ya fadi zabe ba?
Alhaji Tukur: Ah, to wannan duk wani shiri na su da suke barazanar za su yi ni kusan na ce shirme na dauke shi, ni shirme na dauki furucin na su. Duk wani abu daga ubangiji ne, shi mulki ka ce dole sai naka ne zai yi, a’a, ba haka ake nufi ba. Mulkin dimukradiyya ana yin sa ne kan cancanta da kuma waye zai kamata gaskiya da adalci da kuma hada kan al’ummar kasa. Kowace kabila ce matukar dai za ta yiwa jama’ar kasa adalci ba wai kazo ka nuna kazo kai kana mulkin wa ni bangare ba ne.
Aminiya: Kai mazaunin Kurmi ne yaya kallon furucin ’yan asalin yankin game da zaben shekarar 2015?
Alhaji Tukur: To abin da suke nuna dai kusan in ce ta wata karin magana naka sai naka. Su kansu suna hakuri ne da wanna gwamnati ta PDP, amma ba dadinta suke ji ba suna hakuri ne a matsayin dole naka, naka ne.Fatan su dai a samu tsayayye ba sai lalle nasu ko namu ba, wanda dai zai kawo mana ci gaba a kasa ta yadda ba za a samu rikicin addini ko kabilanci ba ko nuna wani bangaranci ba.
Aminiya: Wane fata ko shawara kake da shi ga al’ummar kasar nan?
Alhaji Tukur: Fatana dai Allah Ya sa ayi zaben nan lami lafiya, matasa kuma suyi hattara kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen haddasa tarzomar zabe. A dukufa da yin addu’o’i kan duk wani tashin hankali ko rikici kada Ubangiji ya nuna.