Za a sanya wa dabbobi na’urar sanyaya daki a Italiya
Wasu dabbobi a wani gidan gona da ke kasar Italiya za su samu na’urar sanyaya daki da fanka a dakunan da ake kiwonsu domin magance tsananin zafin da kasar take fama da shi, kamar yadda jaridar La Republica ta bayyana.kasar dai tana fuskanatar matsanancin zafi da ya kai maki 40 na ma’aunin Celsius, wanda masana […]
Wasu dabbobi a wani gidan gona da ke kasar Italiya za su samu na’urar sanyaya daki da fanka a dakunan da ake kiwonsu domin magance tsananin zafin da kasar take fama da shi, kamar yadda jaridar La Republica ta bayyana.
kasar dai tana fuskanatar matsanancin zafi da ya kai maki 40 na ma’aunin Celsius, wanda masana suka ce yana jawo rashin haihuwa a tsakankanin dabbobin. Har ila yau, yanayin zafin yakan sanya shanu su kasa samar da madara kamar yadda suka saba samarwa.
Masana dai sun ce yanayin da ya fi dacewa da dabbobin shi ne lokacin da ma’unin Celsius yake tsakanin maki 22 zuwa 24. “Idan ya dara haka, dabbobi ba sa iya cin abinci sosai, za su sha ruwa mai yawa, sai dai kuma ba za su iya samar da madara ba sosai,” inji su.
A irin wannan yanayi ne zaka ga saniya guda tana iya shan ruwan da ya tasamma lita 140 a rana (kimanin Galan 35 ke nan). Madadin rabin wannan adadin da suke sha a lokacin da yake ba na zafi ba. Hakazalika, ba wai shanu ne kawai abin ke shafa ba, hatta kaji da aladu ma hakan yakan kan shafe su. Bugu da kari, yanayin zafin ya haddasa wutar daji a wasu yankunan kasar.