An sassauta dokar hana ibada a masallatai da coci-coci
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sassauta dokar hana taro a wuraren ibada daga ranar 1 ga watan Yuni. Kwamiti mai yaki da annobar coronavirua na fadar shugaban kasa ne ya shaida haka a bayanan da yake fitarwa a ko wace rana, A cewar kwamitin sassaucin na zuwa ne a karkashin wasu ka’idoji da gwamnatocin jihohi suka […]
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sassauta dokar hana taro a wuraren ibada daga ranar 1 ga watan Yuni.
Kwamiti mai yaki da annobar coronavirua na fadar shugaban kasa ne ya shaida haka a bayanan da yake fitarwa a ko wace rana,
A cewar kwamitin sassaucin na zuwa ne a karkashin wasu ka’idoji da gwamnatocin jihohi suka aminta da su.
Sanarwar tace dokar hana fitar dare da a baya ake farawa daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe za ta koma karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.
Sai dai dokar hana zirga-zirga da jiha zuwa wata jihar za ta cigaba da aiki kamar yadda take a baya.