Za a shafe kwana uku ana marka-marka a jihohin Arewa

Ambaliyar ta fara yin ɓarna a wasu jihohin, inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.

Za a shafe kwana uku ana marka-marka a jihohin Arewa

marka-marka

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin Arewa sakamakon mamakon ruwan marka-marka da za a samu.

Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano da Katsina da Zamfara da Jigawa da Kebbi da Kaduna da Adamawa na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, don haka ta yi kira ga mahukunta a jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.

Tuni ambaliyar ta fara yin ɓarna a wasu jihohin, inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.

Alhaji Bashir Idris Garga, Darakta a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ya ce ruwan saman da za a yi na kwana uku ba ƙakƙautawa zai sa magudanun ruwa da dama da ba a cika damuwa da yashe su ba, su cike wanda hakan ka iya sa ruwan ya malala har ya je ya yi ɓarna.

“Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar ba ta yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba,’’ in ji Garba.

Daraktan ya ce, akwai wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhunhuna a cika da yashi a yi katanga don a canza wa ruwan hanya yadda ba zai shiga ya yi ɓarna ba.

Darakatan ya ƙara da cewa, bayan haka, ya kamata a yashe magudanun ruwa kuma a dage a sanar da ’yan uwa da abokan arziki kan sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗauki matakan riga-kafin lamarin.

Sun kashe yaron da suka sace bayan neman fansar N25m

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT