Za a shirya wa makarantun firamare gasar kacici – kacici a yankin Lere
kungiyar Matasan karamar Hukumar Lere (LELOGYF) da ke Jihar Kaduna, za ta fara shirya wa daliban makarantun firamare na yankin gasar kacici-kacici don karfafa wa daliban gwiwa a kokarin da kungiyar take yi na ba da gudunmawa wajen bunkasa ilimi a yankin.Shugaban kungiyar Abdullahi Hamisu Lati Saminaka ne ya bayyana haka a lokacin da yake […]
kungiyar Matasan karamar Hukumar Lere (LELOGYF) da ke Jihar Kaduna, za ta fara shirya wa daliban makarantun firamare na yankin gasar kacici-kacici don karfafa wa daliban gwiwa a kokarin da kungiyar take yi na ba da gudunmawa wajen bunkasa ilimi a yankin.
Shugaban kungiyar Abdullahi Hamisu Lati Saminaka ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce za su zagaya dukkan makarantun firamaren yankin, su shirya wa daliban gasar kacici-kacici kuma su raba wa daliban da suka nuna hazaka kyaututtuka, don kara musu karfin gwiwa.
Ya ce a kwanakin baya sun gudanar aikin sanya allunan sunayen layuka a yankin domin taimaka wa mutane su san wuraren da suke. “Mun bi unguwanni garuruwan yankin nan mun kafa allunan
sunayen unguwanni da dama don taimaka wa mutane. Kuma mun sanya wani babban alo don maraba da shigowa wannan karamar hukuma a garin Lahadin Maigamo tare da sanya wani a garin Unguwar Bawa,” inji shi.
Ya ce suna ziyartar asibitoci don tallafa wa marasa lafiya da tsabtace asibitocin, kuma suna shirin zagaya asibitocin don ba da gudunmawar jinni ga masu jinya.
Ya ce kungiyar wadda aka kafa ta a shekara ta 2010 a shafin yanar gizo daga baya an fito da ita waje domin bayar da gudunmawa wajen hada kan matasa da kawo ci gaban karamar hukumar.
Ya ce suna da mambobi ’yan asalin yanki a sassn Najeriya da kasashen waje don haka ya yi kira ga matasan yankin su ba su hadin kai da goyon baya domin ba da gudunmawarsu wajen gina karamar hukumar.