Za a soma Gasar Zakarun Turai lami babu Ronaldo da Messi

An yi hasashen cewar Manchester City ce za ta kara lashe kofin Champions League.

Za a soma Gasar Zakarun Turai lami babu Ronaldo da Messi

A Yammacin wannan Talatar ce za a soma Gasar Zakarun Turai ta bana da wasannin cikin rukuni.

Za a soma gasar ce lami babu ’yan wasa biyun da babu kamarsu a tarihin gasar — Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

Bayan lashe kyautar Ballon d’Or sau 12, kofuna marasa adadi da kuma kafa tarihi mai yawa a tsakanin su, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun shiga tarihi a matsayin ’yan wasan kwallon kafa guda biyu da babu kamar su.

Sai dai kuma duk da wannan bajinta, sai ga shi a yanzu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi wadanda babu shakka sun nuna kansu a Turai da taka rawar gani a shekaru da yawa, za a soma kakar bana ba su a Gasar Zakarun Turai.

Hakan dai ya faru ne yayin da Ronaldo wanda shi ne na farko da ya koma taka leda a gasar Saudi Arabia – yana kungiyar Al Nassr – inda shi kuwa Messi ya koma taka ledar Amurka a Inter Miami.

Koda yake akwai fitattun ’yan wasan da babu su a Champions League a kakar nan ciki har da dan kwallon Brazil, Neymar da dan kasar Faransa, Karim Benzema, wanda ya koma Al-Ittihad, shi kuwa Neymar na Al Hilal dukkansu a Saudi Arabia.

Sai dai hankali zai fi karkata kan rashin haskawar Messi da Ronaldo a babbar gasar tamaula ta kungiyoyi, la’akari da har gobe suna ci gaba da jan zarensu a fagen sana’ar ta kwallon kafa.

Idan an waiwaya tarihi, Ronaldo shi ne kan gaba ta fuskar bajinta a Gasar Zakarun Turai, wanda har ake yi wa lakabi da Mista Champions League.

Alkalumma sun tabbatar da cewa Ronaldo wanda ya lashe Kofin Zakarun Turan har sau biyar — daya a Manchester United, hudu a Real Madrid — ya yi wa duk wani takwaransa fintinkau wajen jefa kwallo a raga a gasar.

Ronaldo wanda ya taka leda a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid da Juvenstus, ya fi ko wane dan kwallo yawan buga wasanni (183) a Gasar Zakarun Turai, inda ya jefa kwallo 140.

Haka zalika, Messi wanda ya buga wasanni 163 a Barcelona da PSG, shi ma dai ba a bar shi a baya ba sosai, domin kuwa shi ne dan kwallo na uku mafi yawan buga wasanni a babbar gasar bayan Ronaldo da tsohon golan Real Madrid Iker Casillas da ya haske a wasanni 177.

Ko a yawan cin kwallo, Messi dai shi ke biye wa Ronaldo, wanda a tarihin gasar ya jefa kwallo 129.

Duk da cewa za a soma gasar lami babu wadannan fitattun ’yan kwallo, akwai kuma ’yan kwallon da suke kan ganiya da har ake tsammanin za su iya maye gurbin Ronaldo da Messi bayan sun shude — wato Erling Haaland na Manchester City da kuma Kylian Mbappe na PSG.

Ko wacce wainar za a toya Gasar Zakarun Turai ta bana?

Manchester City wadda ba za ta manta tarihin da ta kafa a birnin Istanbul ba a bayan nan, za ta yi ƙoƙarin kare Kofin Zakarun Turai a makon nan, inda za ta fara wasan rukuni da kulob ɗin Crvena Zvezda ranar Talata.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta wakilci Ingila tare da Arsenal da Manchester United da kuma Newcastle, wadda rabonta da gasar ya kai sama da shekara 20.

Kulob ɗin da ya lashe gasar tamaula ta Scotland, Celtic zai buga gasar zakarun Turai karo na biyu a jere.

Newcastle tana rukuni mai sarƙaƙiya na shida, wanda ya haɗar da Paris St-Germain da AC Milan da kuma Borussia Dortmund.

City na rukuni na uku da ake cewa ba za ta fuskanci ƙalubale ba, da ya ƙunshi RB Leipzig da Red Star Belgrade da kuma Young Boys.

Celtic, wadda ake ganin za ta iya zuwa zagayen gaba, tana rukunin da ya ƙunshi Feyenoord da Atletico Madrid da kuma Lazio.

Manchester United za ta kece-raini a rukunin farko da ya ƙunshi Bayern Munich da FC Copenhagen da kuma Galatasaray.

Arsenal tana rukunin da ya haɗar da ƙungiyar da ta lashe Europa League a kakar da ta wuce, wato Sevilla da kuma PSV Eindhoven da Lens.

Aminiya ta ruwaito cewa, Manchester City ce ta lashe Kofin Zakarun Turan a karon farko bayan doke Inter Milan da ci daya mai ban haushi a wasan da suka fafata a watan Yunin da ya gabata.

Dan wasan tsakiyar City na kasar Sifaniya, Rodri Hernandez ne ya jefa kwallo daya tilo a wasan wadda ta zama mafi muhimmanci a tarihin kungiyar.

Tun kafin lokacin dai an yi ta hasashen cewa City ce za ta yi nasara a wasan la’akari da yadda ta yi wa sa’o’inta zarra a duk gasanni da ta haska a kakar wasanni ta bana.

‘City za ta iya kara lashe kofi’

An yi hasashen cewar Manchester City ce za ta kara lashe kofin Champions League ba wai Real Madrid ko Bayern Munich ba, in ji wata kididdiga daga Gracenote Euro Club Index, wadda ke auna kokarin kungiyoyi a wasanninsu.

City tana da kaso 37 cikin 100 a damar lashe kofin, Real tana da kaso 13 cikin 100 da kuma Bayern mai kaso 11 cikin 100, haka kuma akwai damar wata sabuwar kungiyar ta lashe kofin da kaso 19 cikin 100.

City da Real da Bayern da kuma Barcelona, dukkansu suna da kaso 90 cikin 100 ta kai wa zagaye na biyu a wasannin bana.

Yadda UEFA ta fitar da jadawali

A karshen watan Agustan da ya gabata ne Hukumar UEFA ta fitar da sabon jadawalin Gasar Kofin Zakarun Turai na bana, wanda ke kunshe da kungiyoyi 32 wadanda aka karkasa zuwa rukunnai 8 wato kungiyoyi 4 a duk rukuni guda.

A rukunun A na farko ke nan, akwai kungiyoyin Bayern Munich da Manchester United da FC Copenhagen baya ga Galatasaray.

Rukunin B na kunshe da Sevilla da Arsenal da PSV Eindhoven baya ga RC Lens.

Rukunin C kuwa akwai Napoli da Real Madrid da Braga baya ga Union Berlin.

Rukunin D akwai Benfica da Inter Milan da Salzburg baya ga Real Sociedad.

Rukunin F na kunshe da PSG da Borussia Dortmund baya ga AC Milan da Newcastle United.

Rukunin G akwai Manchester City kana RB Leipzig da kuma Red Star Belgrade kana Young Boys.

Rukunin H kuma na karshe na kunshe da kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da Porto da Shaktar Donetsk da kuma Royal Antwerp.

Dukkanin wasannin rukuni za su gudana ne tsakanin ranar 19 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Disamba, gabanin a tsallaka rukunai daban-daban na gasar a kuma doka wasan karshe a ranar 1 ga watan Yuni da zai gudana a filin wasa na Wembley da ke Landan.

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu