Za a soma karɓar shaidu a shari’ar matashin da ya ƙona masallata a Kano

Ana fargabar cewa yawan waɗanda suka mutu sanadiyyar cinna musu wutar ya ƙaru daga 14 zuwa 19.

Za a soma karɓar shaidu a shari’ar matashin da ya ƙona masallata a Kano

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Unguwar Rijiyar Zaki ta Jihar Kano, ta sanya 4 ga watan Yuli a matsayin ranar soma sauraron shaidu a shari’ar mutumin nan da ake zargi da ƙona masallata a garin Larabar Abasawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa ta jihar.

Ana dai zargin a ranar 15 ga watan Mayu wanda ake ƙara, Shafiu Abubakar Gadan ya yi amfani da man fetur wajen ya cinna wuta kan wasu mutane da ke sallar Asubah a wani masallacin da ke ƙauyen Gadan na Larabar Abasawa a Ƙaramar Hukumar Gezawa, lamarin da ya janyo da yawa daga cikin masallatan sun ƙone yayin da wasu tuni sun riga mu gidan gaskiya.

Sai dai bayan karanto masa ƙunshin tuhumar, wanda ake zargin ya amsa aikata laifukan da ake zarginsa da shi na ɓarna da samar da mummunan rauni da kisan kai da ganganci — laifukan da suka saɓa sashe na 336  da 247 da 221 na Kundin Pinal Kod.

Masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Barista Salisu Tahir, sun shaida wa kotun cewa sun karɓi kwafin shigar da ƙarar daga wurin ‘yan sanda.

Haka kuma, Barista Tahir ya shaida wa kotun cewa, “bisa la’akari da cewa yawan waɗanda suka mutu sanadiyyar sanya wutar ya ƙaru daga 14 zuwa 19.

“Don haka muke roƙon kotu ta ba da wata rana domin gabatar da ƙunshin tuhumar saboda mu sanya haƙiƙanin adadin mutanen da suka mutu sannan kuma mu gabatar da shaidunmu a gaban kotu.”

Aminiya ta ruwaito cewa, Barista Auwal Abubakar daga Hukumar da ke Bayar da Agajin Shari’a ta Ƙasa (Legal Aid) ya shaida wa kotun cewa shi ne zai yi wakilcin wanda ake tuhuma a matsayin lauya mai kariya.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Halhalatul Huza’i  Zakariyya ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Yuli domin soma karɓar shaidu.

Kazalika, Alƙalin ya ba da umarni ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali.