Za a soma yi wa jarirai rigakafin Coronavirus

A baya ba a yi wa yara rigakafin har sai sun kai shekara 5 ko fiye da haka.

Za a soma yi wa jarirai rigakafin Coronavirus

Jaririya

Mahukuntan bayar da magani a Amurka sun sahale cewa yanzu za a iya yi wa jarirai ’yan wata shida rigakafin cutar Coronavirus.

Shugaban Amurkan Joe Biden ya ce iyaye za su iya fara kai yaransu domin rigakafin a cikin makonni masu zuwa.

Amurka ce kasa ta farko a duk fadin duniya da ta amince a yi wa jarirai ‘yan wata shida rigakafin na Coronavirus.

Wannan matakin zai sanya a samar da kananan kwalaben rigakafin ga yara kimanin miliyan 20.

A baya ba a yi wa yara rigakafin har sai sun kai shekara 5 ko fiye da haka.

Shugaban Biden ya bayyana lamarin a matsayin wani muhimmin mataki, wanda zai kara wa iyaye kwanciyar hankali.

BBC ya ruwaito Daraktar Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Amurka, Rochelle Walensky tana cewa iyaye da dama sun zaku a yi wa yaransu rigakafin cutar.

To amma yanzu abin da ya rage a jira shi ne yawan mutanen da za su bukaci a bai wa yaran nasu allurar.

A bara ne aka amince a yi amfani da rigakafin na kamfanin Pfizer a kan yara daga shekara 5 zuwa 11.

Sai dai har yanzu kasa da kashi 30 cikin dari ne kawai na yawan yaran da suka kamata a yi wa rigakafin suka yarda aka yi masu cikakken rigakafin.