Za a ta fara sarrafa ciyawa zuwa abincin dabbobi a Jigawa

Gwamnatin Tarayya ta fara tunani a kan hanyoyin da za a bi wajen yin amfani da ciyawar kachala wajen samar da iskas gas da kuma yin abincin dabbobi da wasu dabarun zamani da aka samu a kan yadda za a sarrafa ciyawar wadda ma’aikatar ruwa ta tarayya ta dauki nauyi. Bayanin hakan ya fito ne […]

Za a ta fara sarrafa ciyawa zuwa abincin dabbobi a Jigawa

Gwamnatin Tarayya ta fara tunani a kan hanyoyin da za a bi wajen yin amfani da ciyawar kachala wajen samar da iskas gas da kuma yin abincin dabbobi da wasu dabarun zamani da aka samu a kan yadda za a sarrafa ciyawar wadda ma’aikatar ruwa ta tarayya ta dauki nauyi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Babban Darakta na Hukumar kogunan Hadejia-Jama’are, Malam Ado Kalid Abdullahi a lokacin wani taro na masu ruwa da tsaki a Hadejia makon da ya gabata. Inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwarta matuka game da yadda ciyawar kachalar ta hana ruwa gudu a cikin kogunan Hadejia-Jama’are, sannan ta kasance barazana ga aikin gona da manoma a arewacin Najeriya, musamman a Jahar Jigawa da makwabtanta.

Kalid ya ce matakin hakan ya biyo bayan yarjejeniya da aka samu tsakanin gwamnatin tarayya da Jami’ar Maryland dake Amurka da Spain da kuma Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da kuma hukumar aikin gona ta kasa wato National Agricultural Edtension Reseach Liason Serbice dake karkashin kulawar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Haka kuma Babban Daraktan Tsare-tsare, Malam Umar Muhammed Kura, ya ce ciyawar ta Kachala ba karamar barazana ba ce ga manoma musamman manoman rani. Ya kuma kara da cewa ciyawar ta na lalata gonaki tare da toshe hanyoyin da ruwa ke wucewa, lamarin dake sa manoman yin asarar amfanin gona mai yawa a duk shekara.

Kura ya ci gaba da cewar daga cikin hekta dubu 12 da 700 da manoma ke nomawa a yankin Hadejia, sun a amfana ne da hekta dubu 5 da 300 ne kacal a lokacin noman damina. “Don haka ne ma gwamnatin tarayya ta gayyato masana akan yadda za a sarrafa ciyawar ta kachala domin al’umma su ci moriyarta maimakon asarar da gwamnatin tarayya take tafkawa, su ma manoman suke tafkawa ta hanyar mayar da ita abincin dabobi da makiyaya za su rika amfani da shi, a lokaci guda kuma hakan zai taimaka wajen magance rikici tsakanin manoma da makiyayan.”

Da yake nasa jawabin, Farfesa Eba na Jami’ar Spain ya bayyana cewa, mafi yawan wadanda gwamnatin tarayya ta nemi hadin gwiwarsu dake manyan jami’o’in duniya manoma ne da suka yi fice akan harkar noma kuma makiyaya ne, sannan masu ruwa da tsaki akan harkar noma wadanda aka gayyato domin bada gudunmawa akan yadda za a sarrafa ciyawar ta kachala ta hanyar amfani da ita wajen yin abincin dabobi da inganta tattalin arzikin kasa.

Shi kuwa Dakta Fernando Eserbano na Jami’ar Maryland dake Amurka cewa ya yi matsalar ciyawar kachala ba ta tsaya a Najeriya ba, matsala ce da ta shafi duniya baki daya, ya ce kasar Senigal da wasu manyan kasashe Afirka suna fama da yaduwar ciyawar ta kachala kuma sun dukufa wajen yaki da ita.

“Muna so mu ji daga bakin manoma kuma mu yi musayar ra’ayi tare da ku, domin hoto daya mai ma’ana ya fi hotuna dubu marasa ma’ana, saboda mayar da ciyawar kachala zuwa wani mataki da zaku anfana zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin manoma a yankin.” In ji shi.