Za a tada ganuwar Kano da ɓuraguzan rusau
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf yace za a yi amfani da ɓuraguzan wuraren da gwamnatinsa ta rushe wurin tada rusasshiyar ganuwar Birnin Kano mai ɗimbin tarihi. Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma umarci jami’an tsaro su hana mutane […]
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf yace za a yi amfani da ɓuraguzan wuraren da gwamnatinsa ta rushe wurin tada rusasshiyar ganuwar Birnin Kano mai ɗimbin tarihi.
Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma umarci jami’an tsaro su hana mutane kwashe ɓaraguzan da sunan cin ganima.
Abba Gida-Gida ya ci gaba da rusau a Kano
Yadda muka tafka asara a rusau din Kano
“Duk waɗanda ba su cikin aikin rusau su nisanci wuraren nan saboda jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wurin ɗaukar mataki a kansu,” in ji Gwamnan.
Kawo yanzu dai an tabbatar da rasuwar aƙalla mutane biyu wurin rububin ‘cin ganima’ a wuraren da sabuwar gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rushewa tun bayan hawa kan mulki a ƙarshen watan Mayu.