Za a tafka mamakon ruwan sama a Kano, Sakkwato da wasu Jihohi 20 – NiMet
Za a fara tafka ruwan ne daga ranar Juma’a mai zuwa
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen za a tafka mamakon ruwan sama a Kano da Sakkwato daga ranar Juma’a.
Hukumar ta kuma ce za a sha ruwan a karin Jihohi 20, kamar yadda ta fitar a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis.
- Tinubu ya yi ta’aziyar rasuwar Sheikh Giro Argungu
- Gwamnan Ondo ya dawo gida bayan sama da wata 3 yana jinya a Jamus
NiMet ta ce a lokacin hasashen, za a tafka mamakon ruwan na tsawon awa 24, kuma za a iya samun tsawa da ’yar kwarya-kwaryar ambaliyar ruwa da iska da walkiya da kuma ambaliya.
A cewar hasashen, za a fuskanci ’yar karamar ambaliya ranar Asabar a Jihohin Ribas da Delta da Bayelsa da Akwa Ibom da Kuros Riba da Yobe da Binuwai da Jigawa da Kano da Katsina da Zamfara da kuma Sakkwato.
“A jihohin Borno da Bauchi da Kaduna da Neja kuwa, akwai barazanar samun ruwan sama kadan-kadan. Dukkan ragowar Jihohin kuma ko dai ba za a sami ruwan ba ko kuma kadan za a yi,” in ji sanarwar.
Ga cikakkun jihohin da za a samu ruwan saman:
Sakkwato
Zamfara
Katsina
Kano
Bauchi
Kaduna
Filato
Oyo
Kogi
Nasarawa
Binuwai
Adamawa
Taraba
Kuros Riba
Imo
Ondo
Edo
Delta
Bayelsa
Ribas