‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14 daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.
Saukar ruwan sama mai karfi
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14 daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.
Cibiyar Gargaɗi Kan Ambaliya (FEWS) ta ma’aikatar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
- Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda
- NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa
Sanarwar, wacce Daraktan Kula da Zaizayar Ƙasa da Ambaliya na ma’aikatar ya fitar, ta gargadi dukkan masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye domin kare kansu.
A cewar sanarwar, garuruwan da jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Kuros Riba (Edor, Ikom, Itigidi, Akpap), Kano (Gwarzo, Karaye), Zamfara (Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukuyum), Taraba (Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gembu, Gun Gun Bodel, Kambari, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Bandawa, Ngaruwa), Abia (Eziama, Umuahia) da kuma jihar Yobe (Geidam, Kanama, Potiskum).
Sauran wuraren sun haɗa da jihar Filato (Langtang, Shendam, Wase), Borno (Ngala), Imo (Okigwe, Otoko) Neja (Sarkin Pawa), Sakkwato (Sakkwato, Wamakko, Isa, Shagari, Makira), Kaduna (Kafanchan) da kuma Akwa Ibom (Oron).
Daga nan sai ma’aikatar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati da su kasance cikin shiri.