Za a tantance masu maganin gargajiya a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta fara tantance masu sana’ar maganin gargajiya a jihar ranar Juma’ar da ta gabata.A jawabinsa na bude taron tantancewar da aka yi a Makarantar Koyon Aikin Jinya, Mashawarcin Gwamnan Jihar Kano a kan Asibitoci Masu Zaman Kansu, Dokta Salisu Ibrahim Tofa ya ce an shirya tantancewar ce da niyyar tsabtace harkar maganin […]
Gwamnatin Jihar Kano ta fara tantance masu sana’ar maganin gargajiya a jihar ranar Juma’ar da ta gabata.
A jawabinsa na bude taron tantancewar da aka yi a Makarantar Koyon Aikin Jinya, Mashawarcin Gwamnan Jihar Kano a kan Asibitoci Masu Zaman Kansu, Dokta Salisu Ibrahim Tofa ya ce an shirya tantancewar ce da niyyar tsabtace harkar maganin gargajiya, ba don tozartawrwa ga masu sana’ar ba. “Manufarmu da wannan tantancewa it ace don a samu gyara a cikin harkar maganin gargajiya, ba don tozartarwa ba. A yanzu haka mun kawo masana harkar daga asibitocin jihar da za su gudanar da tantancewar.”
Ya ce “Idan aka kammala wannan tantancewa za a sanya kowane mai magani a matakin da ya cancanta. Idan gwamnati ta tashi taimaka wa masu maganin za ta taimaka musu ne daidai matakin da kowane mai magani ya taka. Wannan shi ne adalci. Fatanmu shi ne idan mai mgani ya samu kansa a mataki na karshe ya yi kokari ya daga zuwa mataki na gaba.”
Dokta Salisu ya ce za a dauki mako hudu ana gudanar da tantancewar. “Mun raba kananan hukumomin jihar nan gida hudu inda kuma za mu dauki tsawon mako hudu muna gudanar da wannan tantancewa. A kashin farko mun fara da kananan hukumomi 11 da suka hada da Dala da Dawakin Tofa da bagwai da Doguwa da sauransu.”
A jawabin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya ce an shirya tantancewar ce sakamakon bitar da aka shirya wa masu maganin gargajiya a watannin baya. “Daga lokacin da muka shirya bita ga masu maganin gargajiya mun gano al’amura da dama da ya sa muka fito da tsare-tsare ciki har da tantancewar da muke yi a yau. Saboda damuwar gwamnati a kan lafiyar al’ummarta ya sa ta ga dacewar ta ba harkar maganin gargajiya muhimmanci ta yadda za arika samar da magunguna masu inganci.”
Kwamishinan ya yi wa masu maganin albishir cewa gwamnati na shirye-shiryen ganin ta dauki nauyin masu sana’ar maganin gargajiyar zuwa kasashen waje don kara samun gogewa a harkar.
A jawabin Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Babankowa ya nuna matukar godiyarsu ga gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso kan yadda ta yi kokarin hade kawunansu tare da jawo su a jika ba kamar a baya da suke zaune kara zube ba.