Za a tilasta wa mata daura kallabi a Gambiya

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnatin kasar Gambiya ta ce za ta haramta wa ma’aikata mata barin kawunansu babu dan-kwali a wuraren aiki.Wata wasikar sirri da ta fito daga wajen gwamnatin, wacce aka kwarmatawa wata jarida mai zaman kanta, ta bayyana cewa “Dole ne mata ma’aikata su rika daura kallabi ta yadda zai […]

Za a tilasta wa mata daura kallabi a Gambiya
Za a tilasta wa mata daura kallabi a Gambiya

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnatin kasar Gambiya ta ce za ta haramta wa ma’aikata mata barin kawunansu babu dan-kwali a wuraren aiki.
Wata wasikar sirri da ta fito daga wajen gwamnatin, wacce aka kwarmatawa wata jarida mai zaman kanta, ta bayyana cewa “Dole ne mata ma’aikata su rika daura kallabi ta yadda zai rufe kawunansu sosai”, kodayake ba a bayyana dalillin yin hakan ba.
A watan jiya ne Shugaban kasar Yahya Jammeh ya ayyana kasar a matsayin mai bin tafarkin addinin Musulunci, inda ya ce ba za a tilasta  wa kowa kan irin tufafin da zai rika sanya wa ba, kuma mabiya sauran addinai za su iya ci gaba da yinsa ba tare da tsangwama ba. kasar  ta yi fice saboda masu yawon bude ido daga yammacin duniya na kai ziyara a gabar tekunanta.
A shekarar 2013 ne Shugaba Jammeh ya janye kasarsa daga cikin kungiyar kasashen Raunon Birtaniya (Commonwealth), yana mai bayyana  cewa kungiya ce ta ‘yan mulkin-mallaka.