Za a tilasta wa mutane amfani da katin shaidar dan kasa
Nan gaba kadan za a tilasta yin amfani da katin shaida na dan kasa a ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu da sauran cibiyoyin gwamnati domin tantance ma’aikata da kuma cikakken dan kasa.Mukaddashiyar Janar Manajan Hukumar Kula Da Katin Shaidar ’Yan kasa (NIMC), mai kula da sashin shari’a ta hukumar, Hadiza Dagabana ce ta […]
Nan gaba kadan za a tilasta yin amfani da katin shaida na dan kasa a ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu da sauran cibiyoyin gwamnati domin tantance ma’aikata da kuma cikakken dan kasa.
Mukaddashiyar Janar Manajan Hukumar Kula Da Katin Shaidar ’Yan kasa (NIMC), mai kula da sashin shari’a ta hukumar, Hadiza Dagabana ce ta shaida wa manema labarai haka, a Talatar da ta gabata a garin Kalaba.
Ta ce matakin na kunshe ne a cikin dokar sashe na 27 na hukumar NIMC, wato ta samar da katin dan kasa haka nan kuma hukuncin ya tanadi bayar da fasfo na kasa-da-kasa da kuma kula da inshorar lafiya da rajistar katin zabe da makamantansu da ma biyan haraji a ma’aikatun gwamnati da na jihohi. “Daga 9 ga watan Janairu na bana, hukumar za ta fara bin diddigin nuna katin da kuma neman kowane dan Najeriya ya nuna nasa a duk wata ma’amala. Nan ba da dadewa ba hukumar ma za ta nemi hadin kan ma’aikatu da kungiyoyi masu zaman kansu, domin ganin komai ya tafi daidai, ba tare da samun tangarda ba.” Inji ta.
Haka kuma ta bayyana cewa, nan ba da jimawa ba ne hukumar za ta sanar da lokacin da kowa zai je ya karbi katinsa. Dangane da haka sai hukumar ta nemi hadin kan ’yan Najeriya su nuna dattako wajen bayar da duk wasu bayanai ko batu da aka bukata daga gare su. Matukar aka fara amfani da katin, ba za a karbi duk wani uzuri daga wurin wani ba.
Daga karshe, jami’ar ta shawarci ’yan Najeriya su ziyarci cibiyoyin da suka yi rajistar neman katin shaidar, domin karbar katunansu na shaidar dan kasa.