Za a tono gawar basarake bayan watanni 15 da binnewa a Oyo
A ranar Juma’a da ta gabata ce wasu jami’an ’yan sanda daga shiyya ta 11 da ke garin Osogbo, suka isa garin Ilora a Jihar Oyo, domin gudanar da aikin tono gawar wani basarake Onisa na Ilora, Chif Lawrence Owoade, wanda aka yi zargin cewa ya rataye kansa watanni 15 da suka gabata.Mai sarautar, wanda […]
A ranar Juma’a da ta gabata ce wasu jami’an ’yan sanda daga shiyya ta 11 da ke garin Osogbo, suka isa garin Ilora a Jihar Oyo, domin gudanar da aikin tono gawar wani basarake Onisa na Ilora, Chif Lawrence Owoade, wanda aka yi zargin cewa ya rataye kansa watanni 15 da suka gabata.
Mai sarautar, wanda tun a ranar da al’amarin ya afku aka yi masa jana’iza da binne gawarsa, an dakatar da aikin tono gawar tasa a wannan rana, a dalilin rashin bayyanar wasu mutane 9 da ake zargin suna da hannu wajen kashewa da binne shi ba tare da sanar da iyalinsa ba.
Wata majiya mai tushe da aka sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa: “Dole ne a sake tsayar da wata rana da wadannan mutane su 9 za su halarci wajen aikin tonon gawar basaraken, domin gudanar da bincike a game da musabbabin mutuwar tasa tare da mika gawar ga iyalansa domin sake yin kyakkyawar jana’iza da binne shi cikin karramawa amma ba irin jana’izar da aka yi masa a boye a wancan lokacin ba.”
dan uwan marigayi Cif Lawrence Owoade, mai suna Mista Adegboyega Adeniran, ya shaida wa wakilinmu cewa: “Dukkan iyalai da sauran dangin marigayi sun yi matukar bakin ciki da irin yadda aka binne shi a ranar da aka gano gawarsa ba tare da sanar da iyalinsa ba. Wannan abin takaici ne, musamman a matsayinsa na jagoran zuri’ar gidanmu kuma sanannen mutum ne da yake rike da sarautar gargajiya a masarautar Ilora; wanda ya cancanci a yi masa kyakkyawar jana’iza da karramawa a wancan lokaci amma sai aka yi hakan a boye ba tare da saninmu ba. Abin da muke bukata kawai shi ne, a ba mu damar tono gawar dan uwanmu domin sake yi masa jana’iza ta karramawa da girmamawa. Babu ruwanmu da wani bincike a game da musabbabin mutuwarsa. Duk wanda ya aikata wani abu da ya yi sanadin mutwarsa shi da Allah.”
Majiyar ta tabbatar da cewa, kafin mutuwar mamacin a ranar 20 ga watan Nuwamba na shekarar 2014, an yi ta samun sabani a tsakaninsa da wasu mutane da aka boye sunayensu saboda dalilin tsaro, wadanda marigayin ya yi kokarin kai kararsu zuwa kotu da bai cika burinsa ba zuwa ranar da aka samu gawarsa tana lilo a cikin babbar gonarsa da ake zargin cewa shi ne ya kashe kansa. Sai dai majiyar ta ce, ya kamata a binciki wadannan mutane da suka ki halartar wajen tono gawar marigayin kuma dole ne a gudanar da wannan aiki a kan idanunsu idan aka zo zagaye na biyu.
Su dai jami’an ’yan sanda su 6 daga shiyya ta 11 da ke Osogbo, sun koma ne ba tare da ambaton ranar da za su sake dawowa domin aikin tonon kabarin marigayi Onisa na Ilora, Cif Lawrence Owoade ba.