Za a tsare Abba Moro a Gidan Yarin Kuje
Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ce a tsare tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar nan, Mista Abba Moro, a babban Gidan Yarin Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja. A makon jiya ne Hukumar da ke Yaki da yi wa Tattali Arzikin Kasar nan Ta’annati (EFCC) ta cafke shi bisa laifukan […]


Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ce a tsare tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar nan, Mista Abba Moro, a babban Gidan Yarin Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
A makon jiya ne Hukumar da ke Yaki da yi wa Tattali Arzikin Kasar nan Ta’annati (EFCC) ta cafke shi bisa laifukan da ke da alaka da halasta kudin haram da kuma zarginsa da hannu a cuwa-cuwar daukar ma’aikata a shekarar 2014. Abin da ya saba wa dokar daukar aiki.