Za a warware rikicin PDP a makon gobe – Makarfi
Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce yana da yakinin za a warware rikicin jam’iyyar a makon farko na wannan wata na Yuli.Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake bayani kan rikicin na jam’iyyar inda ya ce, a […]
Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce yana da yakinin za a warware rikicin jam’iyyar a makon farko na wannan wata na Yuli.
Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake bayani kan rikicin na jam’iyyar inda ya ce, a matsayinsu na ’ya’yan jam’iyyar masu biyayya kwamitin rikon a shirye yake ya sauka daga shugabanci a duk lokacin da masu ruwa-da-tsaki suka bukaci su yi haka.
Sanata Makarfi wanda ya yi magana a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jam’iyyar na jihohi, ya bukaci tsohon Shugaban Jam’iyyar ta kasa Sanata Ali Modu Sheriff ya rungumi sulhu a matsayin hanyar warware takaddamar da ta taso a jam’iyyar.
Sanata Makarfi ya ce: “Abin da ke faruwa a jam’iyyar abin takaici ne, sai dai kuma abu mai dadi shi ne PDP tana raye, Kuma PDP ce jam’iyyar da jama’a suke so; jam’iyya ce da take kamar wata gwamnati mai jiran gado. Ba domin tana da muhimmanci ba, babu wanda zai rika takaddama a kanta.”
Sai dai tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna bai bayyana za a kawo karshen takaddamar da PDP ke ciki ba zuwa wannan lokaci, sai dai ya ce idan aka bari rikicin ya tsawaita yana iya zama illa ga nasarar jam’iyyar a nan gaba.
Ya ce “Wajibi ne mu kauce wa tsawaita wannan rikici domin hakan cutarwa ce ga jam’iyyar kuma tana iya shafar makomar jam’iyyar na dogon lokaci ba ma ga kokarinmu na ci gaba da rike jihohinmu ba, har ma da sake kwato jihohin da muka rasa tare da karbe mulki a shekarar 2019.”
Sanata Makarfi ya bayyana cewa kwamitin rikon ba an kafa shi ne domin a ci zarafin wani ko a rusa shugabannin PDP na wata jiha ba, sai dai domin a kintsa jam’iyyar don gudanar da babban taronta na kasa tare da samar da hanyar sulhuntawa a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.
Sai ya yaba wa shugabannin jam’iyyar na jihohi kan amincewa da shugabancin kwamitinsa, inda ya ce a matsayinsu na ’ya’yan jam’iyyar ba sun zo ne domin fifita bukatunsu na siyasa ba, kuma ya ba su tabbacin cewa ’ya’yan kwamitin rikon kwaryar a shirye suke su sauka daga mukamansu a duk lokacin da asu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka bukaci haka.
Shugaban Jam’iyyar PDP na yankin Birnin Tarayya, Alhaji Yunusa Suleiman, wanda ya jagoranci shugabannin jihohin ya gabatar wa Makarfi matsayar da shugabannin jam’iyyar na jihohi suka cimma a wani taron da suka yi, inda ya ce shugabannin jam’iyyar na jihohi ba su jin dadin abin da yake gudana a jam’iyyar musamman a matakin kasa.