Za a yaki masu kai wa mahara bayanai a Neja
Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta shirya tsaf domin yakar duk wani mai daukar bayanan sirri yana kai wa ’yan bindigar da suka addabi jihar. Wannan na kunshe ne cikin bayanin da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya fitar a wurin taron kwana daya da aka shirya kan Ta’addanci da Rashin Tsaro a Jihar […]
Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta shirya tsaf domin yakar duk wani mai daukar bayanan sirri yana kai wa ’yan bindigar da suka addabi jihar.
Wannan na kunshe ne cikin bayanin da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya fitar a wurin taron kwana daya da aka shirya kan Ta’addanci da Rashin Tsaro a Jihar Neja, wanda Cibiyar Bincike da Adana Tarihi ta gudanar a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke garin Lapai.
- Mayakan Ansaru sun kashe ’yan bindiga 30 a Kaduna
- Za a hana ’yan kasa da shekara 18 mallakar layin waya a Najeriya
Ya ce, “Abun da masu kai wa ’yan ta’addar ke yi na daukar bayanan sirri yana daga cikin abin da yake kara ta’azzara matsalar tsaro a jihar, wannan ya sa dole muka tsara yadda za a kawar da ’yan bindigar gaba daya da kuma duk masu kai musu bayanai.”
Ya kara da cewa rikicin Fulani da manoma ne farkon abun da ya kawo matsalar tsaro a jihar.
Jihar Neja, da ma wasu jihohi a Arewacin Najeriya na fama da matsalar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.