Za a yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya

Babbar Kotu a Kasar Kenya a yau Laraba za ta yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito. Shari’ar da za ta gudana martani ne kan korafin da wani likita ya gabatar a gaban kotun tun a shekarar 2017. An karrama Buhari da lambar yabo mafi daraja […]

Za a yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya

Kaciyar Mata
Hoto: RFI

Babbar Kotu a Kasar Kenya a yau Laraba za ta yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito.

Shari’ar da za ta gudana martani ne kan korafin da wani likita ya gabatar a gaban kotun tun a shekarar 2017.

A wancan lokacin, likitan ya bayar da hujjar cewa hukuncin haramta yi wa mata kaciya yana cin karo da dokar da ta bai wa kowane jinsin mutane ’yanci da ganin damar abin da za su yi da jikinsu.

Likitan mai suna Dokta Tatu Kamau, ya riki cewa mata suna da damar zuwa asibiti a yi musu wannan al’ada ba tare da fargabar za a kama su ba.

A shekarar 2011 ne Kasar Kenya ta haramta yi wa mata kaciya inda a yanzu ake fargabar wannan kara na iya janyo koma baya ga yunkurin masu fafutikar wannan al’ada ta ci gaba da kasancewa tarihi.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa