‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’
Ko a bara, akalla jihohi 31 ne aka samu rahoton ambaliyar ruwa wacce ta kai ga rasa rayukan mutane da dama tare da shafar mutum miliyan daya da dubu 200.
Ambaliya
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen cewa za a tafka mamakon ruwan sama na tsawon kwana biyar da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a wurare 76 da ke jihohi 19 a Najeriya.
Cibiyar Gargadi kan Ambaliya ta Kasa da ke Ma’aikatar Muhalli ta kasa ce ya yi gargadin ranar Talata, inda ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da ma sauran jama’a da su dauki mataki.
Gargadin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan samun wata mummunar ambaliyar a jihohin Legas da Filato da Anambra da Delta.
- Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano
- Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina
Ana has ashen samun mamakon ruwan saman ne daga daga biyar zuwa tar aga watan Agustan 2025.
Yankunan jihohin da za a iya samun ambaliyar a cewar cibiyar sun hada da Kano (Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Birni da Kewaye, Karaye, Tundun-wada, Wudil, Kunchi); Kebbi (Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa, Gauri-Banza); Neja (Kontagora, Rijau, Ringim); Filato (Mangu); Taraba (Donga, Takum); Jigawa (Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia, Miga); Yobe (Machina, Potiskum); Zamfara (Anka); Sakkwato (Sakkwato, Wamakko); Borno (Biu); da kuma Gombe (Bajoga).
Sauran wuraren sun hada da Akwa-Ibom (Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang); Bauchi (Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a); Ebonyi (Abakaliki, Echara, Ezilo); Kuros Riba (Ogoja Edor, Obubra); Nasarawa (Keana, Keffi, Wamba); Binuwai (Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya); Kaduna (Jaji, Kafancha, Birnin-Gwari, Zaria) sai kuma a jihar Katsina (Bindawa, Bakori, Daura, Funtua).
Ambaliyar ruwa dai ta zama wata babbar annoba da ke faruwa a Najeriya a kowacce shekara inda takan lalata dukiyoyin da ma rasa rayukwan jama’a.
Ko a bara, akalla jihohi 31 ne aka samu rahoton ambaliyar ruwa wacce ta kai ga rasa rayukan mutane da dama tare da shafar mutum miliyan daya da dubu 200.