Za a yi ambaliyar ruwa a Kano da wasu jihohin Arewa 12 – NEMA
Hukumar ta ce dukkan jihohin a Arewacin Najeriya suke
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana wasu yankuna 50 a Jihohin Arewa 13 da ta ce za su fuskanci ambaliyar ruwa cikin kwanaki 4 masu zuwa.
A cewar hukumar, ana hasashen fuskantar ambaliyar ce daga ranar Laraba, 13 zuwa Lahadi 17 ga watan Satumban 2023.
- Zargin karkatar da hatsi: Gwamnan Kano ya dakatar da shugaban kamfanin KASCO
- Larabgana: Asali da tarihinta a al’adar Bahaushe
Ko’odinetan hukumar a Jihar Legas, Ibrahim Farinloye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Legas, ranar Laraba.
A cewar sanarwar, a Jihar Kano, ana hasashen samun ambaliyar a yankunan Sumaila da Kunchi.
A jihar Kebbi kuwa, akwai yankin Argungu, sai Katsina mai yankunan Bindawa, Jibiya, Kaita da cikin birnin Katsina.
Sauran yankunan su ne Kwantagora da Mashegu da New Bussa a jihar Neja, sai Kosubosu a Kwara.
“A Zamfara, akwai yankunan Kauran Namoda da Shinkafi; sai Bauchi mai yankunan Bajoga, Darazo, Kirfi, Azare, Jama’are, Itas, Misau; Taraba na da yankunan Bali, Donga, Lau, Serti, Mutum-Biyu, Yorro, yayin da a Borno akwai yankunan Briyel, Biu, Dikwa, Kukawa,” in ji shi.
Ya kuma ce a jihohin Adamawa kuwa, yankunan da ake hasashen fuskantar ambaliyar su ne Ganye, Mubi, Demsa, Jimeta, Mayo Belwa, Numan, Shelleng, da Song.
Farinloye ya kuma ce a Yobe, akwai yankunan Dapchi, Gashua, Geidam, Kanamma, Machina da Potiskum da su ma ke cikin barazana.
A Gombe ma, NEMA ta ce za a iya samun ambaliyar a Nafada, sai Jigawa mai yankunan Dutse, Gumel, Gwaram da Miga.
Ko’odinetan ya kara da cewa sakamakon ƙaruwar yawan ruwa a Kogin Kwara da na Binuwai, ana shawartar mazauna yankunan da ke makwabtaka da kogunan har zuwa jihar Bayelsa da su ma su dauki matakan kariya. (NAN)