Za a yi amfani da dabbobi don hasashen girgizar kasa

A farkon watan nan ne masana kimiyya a kasar China suka bude cibiyoyin bincike guda bakwai domin hasashen lokacin faruwar girgizar kasa. Galibin cibiyoyin suna gidajen zoon garin Nanjing da ke gabashin lardin Jiangsu, kamar yadda kafar yada labarai ta Modern Edpress ta wallafa a shafinta na Intanet.Masanan sun ce za su sanya ido a […]

Za a yi amfani da dabbobi don hasashen girgizar kasa
Za a yi amfani da dabbobi don hasashen girgizar kasa

A farkon watan nan ne masana kimiyya a kasar China suka bude cibiyoyin bincike guda bakwai domin hasashen lokacin faruwar girgizar kasa.

Galibin cibiyoyin suna gidajen zoon garin Nanjing da ke gabashin lardin Jiangsu, kamar yadda kafar yada labarai ta Modern Edpress ta wallafa a shafinta na Intanet.
Masanan sun ce za su sanya ido a kan sauyin dabi’un dubban dabbobi, wanda hakan a cewarsu zai taimaka wajen gano hakikanin lokacin faruwar musibar girgizar kasa.
A wani gidan zoo da ke birinin Yuhuatai na kasar, an killace kaji akalla guda dubu biyu da aladu 200 da sauran dabbobi da dama. Har ila yau, an kakkafa kemarori da dama, wadanda za su dinga daukar hotunan dabbobin da ke gidan a kodayaushe. Bugu da kari, ma’aikatan gidan za su mika rahoton dabi’un dabbobin, sau biyu a kullum, ga wani babban jami’i a cibiyar binciken don yin nazari.
Babban Jami’in Cibiyar, mai suna Zhao Bing, ya ce dabbobi suna shiga wani yanayi na damuwa gabanin lokacin faruwar girgizar kasa.
An shafe lokaci mai tsawo da yin amannar cewa wasu daga cikin dabi’un dabbobi na iya samar da wani haske game da lokacin faruwar iftila’in. A shekarar 2011, binciken wasu masana kimiyya ya nuna cewa sauyin wasu sinadarai da ke cikin kasa na iya taimaka wa wasu dabbobi wajen hango karatowar girgizar kasa. Binciken nasu ya samu tagomashi sosai a idon jama’a bayan wani rahoto ya tabbatar da cewa gungun wasu kwadi sun kauracewa muhallinsu a birnin L’Akuila na kasar Italiya, kwanaki kadan gabanin faruwar mummunar girgizar kasa a birnin, wadda ta cinye rayukan mutum 308.