Za a yi amfani da na’ura wajen tantance shigar kwallo raga a gasar cin kofin duniya na mata
Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayar da sanarwar fara amfani da na’urar da ke tantance shigar kwallo raga (Goal-line technology) a gasar cin kofin duniya na mata da za a yi a watan Yuni mai zuwa a Kanada. Hukumar ta ce za ta fara amfani da na’urar ce a wannan karo, bayan […]
Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayar da sanarwar fara amfani da na’urar da ke tantance shigar kwallo raga (Goal-line technology) a gasar cin kofin duniya na mata da za a yi a watan Yuni mai zuwa a Kanada.
Hukumar ta ce za ta fara amfani da na’urar ce a wannan karo, bayan an samu nasarar amfani da ita a gasa daban-daban da Hukumar ta shirya a baya. An yi amfani da na’urar a gasar Club World Club a shekarar 2012 da gasar Confederation Cup a shekarar 2013 da kuma a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ya gudana a Brazil a bara.
Tun a watan Disambar bara ce dai Hukumar ta gayyaci kamfanin da ke alhakin dasa na’urar don yiwuwar dasa na’urar a filayen wasanni na Edmonton da na
Moncton da Montreal da Ottawa da bancouber da kuma na Winnipeg da ke Kanada.
Wannan shi ne karon farko da za a fara amfani da na’urar a wasan kwallon kafa na duniya a bangaren mata.