Za a yi binciken fashewar tukunyar gas a madatsar ruwa ta Jos
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong sun bayar da umarnin a gudanar da bincike kan fashewar tukunyar adana gas din Chlorine da Hukumar Ruwa ta Jihar Filato ke amfani da shi wajen tace ruwa a matatar ruwa ta Lamingo da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu da ta yi bindiga a […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong sun bayar da umarnin a gudanar da bincike kan fashewar tukunyar adana gas din Chlorine da Hukumar Ruwa ta Jihar Filato ke amfani da shi wajen tace ruwa a matatar ruwa ta Lamingo da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu da ta yi bindiga a ranar Asabar da ta gabata, inda ta hallaka mutum takwas tare da raunata fiye da mutum 100.
Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya mika ta’aziya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su tare da nuna takaici kan faruwar hadarin.
Gwamnan Lalong ya ce an shawo kan lamarin tare da daukar matakan ganin lamarin bai shafi ruwan da ake tacewa a tura wa jama’ar birnin Jos ba. Ya ce “Mun bayar da umarni a sauya duk kayan aikin da suka tsufa a matatar ruwan,” inji Gwamnan.
Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum takwas sun rasu inda mutum 112 suka samu rauni a hadarin.
Da yake zantawa da ’yan jarida kan hadarin, Ko’odinetan Hukumar NEMA a shiyyar Arewa ta Tsakiya, Abdulsalami Mohammed ya ce baya ga mutanen da suka rasu da wadanda suka ji rauni, fashewar tukunyar ta kone gidajen jama’a da ke makwabtaka da matatar ruwan. Ya ce wadanda suka ji rauni a hadarin suna kwance a Asibitin Koyawa na Jami’ar Jos da Asibitin Jan-Kwano da Asibitin kwararru na Jos da kuma Asibitin OLA.
Ya ce hadarin wani babban abin takaici ne, don haka za a sauya matsuguni ga mutanen da suke zaune a kusa da matatar don guje wa sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.