Za a yi daurin rai da rai ga masu fyade a Osun
Majalisar Dokokin jihar Osun ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu aikata laifin fyade a jihar. Haka kuma ta amince a daurin shekaru 14 ga duk wanda aka samu da laifin yunkurin yin fyade. Shugaban Majalisar Rt. Hon. Timothy Owoeye ya ce dokar wadda a baya aka bai wa jama’ar jihar damar […]
Majalisar Dokokin jihar Osun ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu aikata laifin fyade a jihar.
Haka kuma ta amince a daurin shekaru 14 ga duk wanda aka samu da laifin yunkurin yin fyade.
Shugaban Majalisar Rt. Hon. Timothy Owoeye ya ce dokar wadda a baya aka bai wa jama’ar jihar damar bayyana ra’ayinsu a kai, za ta taimaka wajen magance matsalar yawaitar fyade a jihar.
- Za a rataye wanda ya kashe ’yar shekara 3 ta hanyar fyade
- Majalisar Tarayya ta yi watsi da hukuncin dandake masu fyade
Za kuma ta ba wa mahukunta kwarin gwiwar hukunta masu laifin tare da hana matasa fadawa cikin mummunar dabi’ar ta fyade, a cewarsa.
“Don haka ina gargadin matasa da su guji dabi’ar nan ta yin kudi a dare daya. Bai dace a rika musguna wa mata ba ko kadan” inji shi.
A karshe Shugaban Majalisar ya yi kira ga matasa su rike ayyukan dogaro da kai domin guje wa shiga miyagun ayyuka.