Za a yi facin titin Abuja zuwa Tafa a kan miliyan N366

Za a kammala aikin fadinsa sauran gyare-gyaren cikin makonni biyu

Za a yi facin titin Abuja zuwa Tafa a kan miliyan N366

Gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar facin wani ɓangare na titin Abuja zuwa Kaduna a kan Naira miliyan 366.

Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa ta ce za a kashe Naira miliyan kan366 ne wajen yin faci da kuma gyara wuraren da suka lalace a titin daga Zuba da ke Babban Birnin Tarayya zuwa Ƙaramar Hukumar Tada da ke Jihar Neja.

Aikin mai tsawon kilomita 31 zai tsaya ne Mahaɗar Dikko Junction da ke iyakar Jihar Neja da Kaduna, kuma ana sa ran kammala shi cikin makonni biyu.

Kamfanin da aka ba wa aikin facin titin, H&M Nigeria Limited, ya riga ya kai kayansa wurin tun ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, 2024.

A yayin ziyarar gani da ido da suka kai wajen, Daraktan Kula da Manyan Hanyoyin Yankin Arewa ta Tsakiya, Injiniya Mohammed Goni da takwaransa mai kula da ayyuka na musamman a yakin Arewa, Injiniya Olufemi Adetunji, sun bukaci kamfanin ya tabbatar ya aiwatar da aikin gyaran, yadda aka tsara kuma a cikin lokaci.

Injiniya Goni ya ba da tabbacin cewa da zarar an kammala aikin, za a ba da kwangilar gyaran ɓangaren da aya tashi daga Tafa zuwa Kaduna.

Yanzu ahekara shida ke nan kamfanin Julius Berger ke aikin gyaran babban titin Abuja zuwa Kaduna, ba tare da ya kammala ba.

Yanayin lalacewa da ramukan da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna mai tsawon kilomita 180 ya mayar da hanyar tamkar tarkon mutuwa ga matafiya.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya