Za a yi gasar Tenis ta duniya a watan gobe a Jihar Legas

Hukumar kwallon Tenis ta kasa da kasa ta kammala shirye-shirye don gudanar da gasar kwallon Tenis ta duniya a cikin watan Maris mai zuwa a Jihar Legas. Ana sa ran hukumar wasanni ta tarraya ita za ta karbi bakuncin wasan Tenis din wacce aka yi mata taken ‘Bude Legas’ inda kwarrarun ’yan wasan da suka […]

Za a yi gasar Tenis ta duniya a watan gobe a Jihar Legas
Za a yi gasar Tenis ta duniya a watan gobe a Jihar Legas

Hukumar kwallon Tenis ta kasa da kasa ta kammala shirye-shirye don gudanar da gasar kwallon Tenis ta duniya a cikin watan Maris mai zuwa a Jihar Legas.

Ana sa ran hukumar wasanni ta tarraya ita za ta karbi bakuncin wasan Tenis din wacce aka yi mata taken ‘Bude Legas’ inda kwarrarun ’yan wasan da suka shahara a duniya za su fafata.
Hukumar kwallon Tenis ta kasar Egypt za su halarci gasar da kwararrun ’yan wasa 10 don su fafata a gasar don lashe kyaututtukan da aka sanya.
kwararrun ’yan wasan Tenis na Egypt da suka hada da Omar Assar da Nadeen El-Dawatly za su halarci gasar inda za su kare kambinsu.
Omar Assar shi ne ya lashe gasar a shekarar 2013 bayan da ya lallasa fitaccen dan kwallon Tenis na Najeriya mai suna Segun Toriola.
Assar ya ci gaba da rike kambunsa a shekarar 2014 bayan da ya yi nasara a kan abokin karawarsa El-Sayed Lashin.
Omar wanda ya lashe gasar Tenin ta kwararru na Afirka a birnin Cairo ya ce yana son ganin ya zo Legas don ya kare kambunsa.
‘Ina mutukar son ’yan kallon jihar Legas saboda zuwan da na yi Najeriya sau biyu na ji dadin wasan da na yi saboda yadda ’yan kallo suka rika goya mini baya. Saboda haka zan dawo Najeriya na kare kambuna saboda ina mutukar son kambun’. Inji shi.
Ya kara da cewa ‘Ba makawa zan zo Legas saboda gasar ta zama jinin jikina shi ya sa na zaku na zo na nishadantar da kaina. Na san gasar ba za ta zama abu mai sauki a gare ni ba saboda Najeriya tana da kwararrun ’yan wasa’.
Ita kuwa El-Dawatly wacce ta lashe gasar Tenis ta kwararrun kasashen Afirka bangaren mata ta ce tana sa ran zuwa jihar Legas don ganin ta lallasa abokiyar karawarta Dina Meshref.