Za a yi gwajin motocin haya masu amfani da lantarki a Ingila 1

Za a fara gwajin motocin haya da za su yini suna aiki da wutar lantarki a Ingila, inda a cikin watan Janairun nan wadansu sababbin motoci guda takwas masu aiki da wutar lantarki za su fara aiki a garin Milton Keynes.Motocin za su jima suna aiki ne saboda za su rika samun cajin batirinsu a […]

Za a yi gwajin motocin haya masu amfani da lantarki a Ingila 1

Za a fara gwajin motocin haya da za su yini suna aiki da wutar lantarki a Ingila, inda a cikin watan Janairun nan wadansu sababbin motoci guda takwas masu aiki da wutar lantarki za su fara aiki a garin Milton Keynes.
Motocin za su jima suna aiki ne saboda za su rika samun cajin batirinsu a tashoshin farko da na karshe a hanyarsu ta hanyar wadansu fayafayan caji da aka manna kan kwalta.
Wannan shi ne karo na farko a fadin Ingila da za a yi amfani da irin wadannan motoci masu amfani da baturan da ake cajinsu maimakon amfani da man fetur ko dizel.
Motocin dai za su rika zirga-zirga ne kan wata hanya mai nisan kilomita 25 tsakanin unguwannin Wolberton da Bletchley na garin Milton Keynes, inda za su rika daukar fasinjoji dubu 800 a kowace shekara.
Bayan caji da daddare a tasha, motocin za su rika caji a farko da karshen hanyar. Motocin za su rika tsayawa ne a kan wadansu fayafayan caji da aka manna kan kwalta. Daga nan direban zai saukar da wani faifai da ke kasar motar wanda zai rika karbar cajin a cikin mintuna 10 motar za ta koma bakin aiki. Wannan tsarin na rashin na rabe maimakon joni zai taimaka wurin caja batirin motar cikin hanzari.
Tuni dai aka fara amfani da irin wannan tsarin cajin a garuruwan Turin da Genoa na Italy, Utrecht na Netherlands da Mannheim a Jamus.
A bara, an dwata hanya a Koriya ta Kudu mai nisan kilomita 12 wacce ke caja batirin motoci masu amfani da wutar lantarki ba tare da sun tsaya ba. A garin Gumi da ke kasar Koriyar kuma akwai motocin haya biyu da ke amfani da wutar lantarki.