Za a yi jana’izar alhazan kasar Jordan 41 a Makkah
Ana ci gaba da neman sauran mahajjatan kasar Jordan 22 daga cikin 106 da suka bata a Saudiyya
Gwamnatin kasar Jordan ta ce za a gudanar da jana’izar alhazan kasar guda 41 a birnin Makkah, bayan sun rasu a sakamakon tsananin zafi a lokacin aikin hajji a kasar Saudiyya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jordan, Sufian Qudah, ya sanar cewa kasar an gano 84 daga cikin alhazan kasar 106 da suka bace a Saudiyya.
Qudah ya bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun ba da kulawar da ta dace ga alhazan 84, wadanda wasunsu ke cikin mawuyacin hali.
Ya kara da cewa, ofishin jakadancin kasar da ke Makka na kara ba da kula tare da sanya ido kan halin da alhazan ke ciki tare da hadin gwiwan hukumomin Saudiyya.
- Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall
- Alhajin Filato ya rasu a Makkah
- DAGA LARABA: Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau
Kakakin ya ci gaba da cewa har yanzu ana ci gaba da neman sauran alhazan kasarsa 22 da suka bata.
Daga nan ya yi kira ga dukkan ’yan kasar da ke Hajji da su tuntubi ma’aikatar idan ana bukatar taimako, ciki har da kai rahoton wadanda suka bace ko kuma jigilar gawarwakin, idan sun mutu.