Za a yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Ƙasa a ranar Juma’a 

Ɗan uwansa ya ce sojoji ba su bayar da gawar mamacin ba, amma a cewarsa suna sa ran yi masa jana’iza a ranar Juma’a.

Za a yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Ƙasa a ranar Juma’a 

Za a yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Abuja, a ranar Juma’a.

Babban yayansa, Moshood Lagbaja ne, ya bayyana haka yayin ziyarar ta’aziyya da Ƙungiyar Ɗaliban Makarantar St. Charles Grammar School Osogbo (SCOBA) suka kai masa a Jihar Osun.

Moshood, ya ce har yanzu sojoji ba su bai wa iyalansa gawarsa ba, amma ya tabbatar da cewar za a yi jana’izarsa a ranar Juma’a.

Ƙungiyar SCOBA ta gabatar da takardar ta’aziyya ga iyalan, wanda Shugaban ƙungiyar, Tade Adekunle, ya sanys wa hannu.

Ƙungiyar ta bayyana Lagbaja a matsayin abun sha’awa, kuma jarumin soja da ya yi wa ƙasa hidima.

“Muna cikin jimami da rashin wannan babban mutum, wanda ya kasance abin alfahari a gare mu kuma jajirtaccen shugaba.

“Rayuwar Laftanar Janar Lagbaja, sadaukarwarsa da abun da ya bari, suna ba mu ƙwarin gwiwa.

“Yana da tasiri a tsakanin al’ummarmu a lokacin rayuwarsa. Ubangiji Ya ba mu haƙurin rashinsa.

“Muna fatan Ubangiji ya ba ku zuciyar daure wannan rashi.

“Ubangiji Ya sa kyawawan abubuwan da Laftanar Janar Lagbaja ya yi, hikimarsa, da nasarorinsa su zama abin tunawa a zukatanku, kuma rayuwarsa ta zama abin koyi ga al’umma masu zuwa.”

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa