Za a yi jana’izar jagoran addinin Iran Ali Khamenei a watan Yuli
Jana’izar ƙasar da za a gudanar a ranar 4 ga Yuli za ta zo daidai da Ranar ’Yancin Amurka, wadda a bana ta cika shekara 250 da kafuwa.
Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya sanar da cewa za a gudanar da jana’izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya jagoranci ƙasar tsawon kusan shekara 37 kafin rasuwarsa a harin sama da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar 28 ga Fabrairu.
Rahotanni daga Iran sun ce tun farko an shirya gudanar da jana’izar ce a watan Maris, amma aka ɗage ta sakamakon yaƙin da ya dabaibaye ƙasar a lokacin.
- Fiye da ƙungiyoyi 60 sun yi zanga-zanga kan taron G7 a Faransa
- Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno
A cewar rahotannin, za a gudanar da jana’izar ce ta tsawon kwanaki shida, daga ranar 4 zuwa 9 ga Yuli.
Za a fara da jana’izar ƙasa a babban birnin Tehran daga ranar 4 zuwa 6 ga Yuli, sannan a ci gaba da wasu bukukuwan girmamawa a birnin Qom, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin addini na ƙasar.
Daga bisani, za a binne marigayin a ranar 9 ga Yuli a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, wanda shi ne garinsu na haihuwa.
Jana’izar ƙasar da za a gudanar a ranar 4 ga Yuli za ta zo daidai da Ranar ’Yancin Kan Amurka, wadda a bana ta cika shekara 250 da kafuwa.
Bayan rasuwar Ali Khamenei, ɗansa Mojtaba Khamenei ya gaje shi a matsayin Jagoran Koli na Iran a farkon watan Maris, inda ya zama mutum na uku da ya riƙe muƙamin tun bayan kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1979.
Rahotanni sun ce Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa da wasu manyan jami’an ƙasar. Sai dai tun bayan naɗa shi, bai fito bainar jama’a ba, kuma ana fitar da saƙonninsa ne ta hanyar sanarwar da ake danganta masa.