Za a yi jana’izar mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi bayan Azahar

Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi ta rasu a yammacin ranar Lahadi a wani asibiti.

Za a yi jana’izar mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi bayan Azahar

Sheik Ahmad Gumi

Mahaifiyar fitaccen malamin addinin Musulunci nan mazaunin Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ta rasu.

Sheikh Ahmad Gumi ya sanar cewa mahaifiyar tasa ta rasu ne a wani Asibiti da ke garin Abuja da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Yau ina cikin alhinin ina sanar da rasuwar mahaifiyata…; Don Allah a roka mata gafara da rahamar Allah.

“Maganar karshe da ta yi min makonni uku da suka wuce ita ce,  ‘in sha’a Allahu, Allah Zai sada ta da ’ya’yanta da jikokinta a Aljannah’.

“Wadannan kalaman sun kara min kwarin gwiwa; Allah Ya kai rahamarsa gare ki. Amin,” kamar yadda ya wallafa.

Malamin ya sanar cewar za a yi jana’izarta da misalin karfe 1 na rana a ranar Litinin bayan Sallar Azahar a gidan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Unguwar Sarki GRA, bayan Lugard Hall, Kaduna.