Za a yi karon batta tsakanin Spain da Croatia a wasan karshe na Nations League

Italiya za ta hadu da Netherlands don neman gurbin na 3 a gasar Nations League.

Za a yi karon batta tsakanin Spain da Croatia a wasan karshe na Nations League

Za a yi katon batta tsakanin Croatia da Spain a wasan karshe na gasar Kofin Kasashen Turai wato Nations league.

Lamarin na zuwa ne bayan da Spain ta yi nasarar doke abokiyar karawarta Italiya da kwallaye 2 da 1 a ranar Alhamis.

Yayin haduwar ta jiya dai, kwallon Joselu ce ta kai Spain ga nasara a minti na 88 da fara wasa, bayan da tun farko Pino ya zura kwallo a minti na 3 da sanya wasa ko da bada jimawa ba Italiya ta farke ta hannun Immobile a bugun fenaretin da ta samu.

Nasarar ta jiya na nuna cewa, Spain wadda ta shafe tsawon shekaru ba tare da kai wata lambar yabo gida ba, ta kama hanyar zama zakarar ta Nations League, ko da ya ke tana fuskantar babban kalubale daga Croatia wadda ke fatan kai kofi gida karon farko a tarihi.

Ita ma dai Spain rabonta da kai kofi gida tun shekarar 2012 wanda ke nuna cewa za ta yi iyakar kokarinta wajen lashe wannan kofi, kamar yadda dan wasanta na tsakiya Rodri da ya kai Manchester City ga lashe Kofin Zakarun Turai ke cewa za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin abin da ya faru a 2021 bai sake faruwa ba.

A ranar Lahadi ta jibi dai za a barje gumi a filin wasa na Stadion Feijenoord ‘De Quip’ da ke Rotterdam a kasar Holland.

Jerin wadanda za su yi alkalancin wasan karkashin jagorancin Stefan Lupp sun hada da  Marco Achmüller da Marco Fritz da Sven Jablonski da Stuart Attwell da kuma  Ivan Kružliak.

A bangare guda Italiya za ta hadu da Netherlands don neman gurbin na 3 a gasar ta Nations League.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa