Za a yi kiɗan ƙwarya da na shantu yayin auren zawarawa a Kano – Daurawa
Sai dai ya ce ba za a bar mutane su shiga wajen shagalin da waya ba
Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske a kan shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 1,800 da gwamnatin Jihar ke kokarin yi.
- Ɗan Najeriya na yunkurin kafa tarihin yin maganar awa 120 babu tsayawa
- Za a tafka mamakon ruwan sama a Kano, Sakkwato da wasu Jihohi 20 – NiMet
A cewar Sheikh Daurawa, za a yi shagulgula iri-iri domin nishadantar da ma’auratan, tun da a cewarsa, addinin Musulunci bai hana ba.
Ya ce, “Za mu gayyato masu kidan ƙwarya da na shantu da duk wani nau’i na nishadi da Musulunci ya amince da shi.
“Amma ba za mu bar kowa ya shiga da waya ba saboda kada a ɗauki matan mutane suna nishadi,” in ji shugaban na Hisbah.
Ya kuma ce sun ware wa kowacce daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar 44 Naira dubu 500 domin shagulgulan nishadi a yayin biki.
Gwamnatin Jihar dai ta ware sama da miliyan 800 domin bikin zawarawan.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta sanar da ranar da za a yi bikin ba, amma ta ce tana ci gaba da shirye-shirye.