Za a yi kuri’ar raba gardama a Rwanda

Hukumomi a kasar Rwanda sun ce za a yi kuri’ar raba- gardama domin bai wa Shugaba Paul Kagame damar yin ta-zarce a karo na uku, kamar yadda BBC ya bayyana.Hukumomin sun ce za a kada kuri’ar ce a ranar 18 ga watan nan.A watan jiya ne dai ’yan Majalisar Dokokin kasar suka amince su sauya […]

Za a yi kuri’ar raba gardama a Rwanda
Za a yi kuri’ar raba gardama a Rwanda

Hukumomi a kasar Rwanda sun ce za a yi kuri’ar raba- gardama domin bai wa Shugaba Paul Kagame damar yin ta-zarce a karo na uku, kamar yadda BBC ya bayyana.
Hukumomin sun ce za a kada kuri’ar ce a ranar 18 ga watan nan.
A watan jiya ne dai ’yan Majalisar Dokokin kasar suka amince su sauya kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa Mista Kagame damar sake yin takara bayan mutum miliyan uku sun yarda da hakan.
Ana yaba Shugaba Kagame game da aikin da ya yi na sake gyara kasar bayan kisan kare-dangin da aka yi a 1994, sai dai ’yan hamayya sun ce mutum ne da ba ya jure irin sukar da ake yi wa gwamnatinsa.
Akalla mutum dubu 800 ne suka rasu galibi ’yan kabilar Tutsi da Hutu lokacin rikicin.
Sai dai shugaban bai bayyana ko zai tsara takara a zaben shekarar 2017 ko a’a ba, amma ya ce zai bayyana hakan ne bayan kammala kuri’ar raba-gardamar.