Za a yi sallar roƙon ruwa a Saudiyya

Sarki Salman bn Abdulaziz na Saudiyya ya yi kira da a gudanar da sallar roƙon ruwa a faɗin ƙasar baki ɗaya a gobe Alhamis. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da gidan sarautar ƙasar ya fitar a jiya Talata. Kotun ta bai wa EFCC umarnin tsare Yahaya Bello ’Yan daba sun kashe ɗan sanda da […]

Za a yi sallar roƙon ruwa a Saudiyya

Sarki Salman Bin Abdulazeez na Saudiyya

Sarki Salman bn Abdulaziz na Saudiyya ya yi kira da a gudanar da sallar roƙon ruwa a faɗin ƙasar baki ɗaya a gobe Alhamis.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da gidan sarautar ƙasar ya fitar a jiya Talata.

Sarkin ya yi kiran da a yi sallar ta Istisqa, kamar yadda yake a Sunnar Annabi Muhammad (SAW), idan ana cikin buƙatar ruwan sama.

Haka kuma Sarkin ya buƙaci dukkan Musulmi da su yi addu’o’in neman gafara da tuba ga Allah (SWT), kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Sudiyyar ya ruwaito a sanarwar.

Sannan kuma ya yi kira ga jama’a su ƙara abubuwa na alheri da neman kusanci ga Allah (SWT), kamar sadaka da addu’o’i don neman rahama da sauƙin rayuwa da kuma jinƙai daga Ubangiji.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa