Za a yi taron zamanantar da Karatun Tsangaya a Kaduna

Hukumar Kula da Nazarin Karatun Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS) za ta gudanar da taron kara wa juna sani a kan karatun Tsangaya, a ranar 21 ga Disamba, 2020. Mukaddashin magatakarda na hukumar, Farfesa Muhammad Shafi’u Abdullahi ya ce, taron zai maida hankali ne wajen hada kawunan Malamai da Daliban Tsangaya, don zamanantar […]

Za a yi taron zamanantar da Karatun Tsangaya a Kaduna

Hukumar Kula da Nazarin Karatun Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS) za ta gudanar da taron kara wa juna sani a kan karatun Tsangaya, a ranar 21 ga Disamba, 2020.

Mukaddashin magatakarda na hukumar, Farfesa Muhammad Shafi’u Abdullahi ya ce, taron zai maida hankali ne wajen hada kawunan Malamai da Daliban Tsangaya, don zamanantar da karatun.

A cewarsa, “taron farko da hukumar ta yi a Kano domin jawo hankalin malamai da daliban Tsangayu domin tofa albarkacin bakinsu, amma sai dai wakilan gwamnatin Kano sun yi watsi da shirin hukumar.

Almajirai na karatu a makarantar Allo

“An sake yin irin wannan taro a Bauchi, har Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya harlarci taron, kuma ya ba mu tabbacin ba da gudunmawarsa don zamanantar da harkar kararun Tsangaya.

“A Ilorin ma an yi irin wannan taron inda aka zabo malamai da Alaramommi daga kudu maso yammacin kasar nan don nemo mafita,” a cewarsa.

Ya kara da cewa gudunmawar da malamai da alaramommi za su bayar a yayin taron na da matukar muhimmanci wajen kawo hadin kai ga tafiyar.