Za a yi wa dan Majalisar Tarayyar Yobe Kiranye
Al’ummar Mazabar Ngazargamu daga Jihar Yobe, za su yi wa dan Majalisarsu na Tarayya, kiranye kan watsi da su
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Ngazargamu daga Jihar Yobe, Lawan Shettima Ali, na fuskantar barazanar kiranye daga al’ummar mazabarsa.
Honorabul Lawan Shettima Ali ya gamu da fushinsu ne kan zargin da suke masa na watsi da su tun da suka zabe shi.
A tattaunawar da suka yi da Aminiya, wasu jagororin Mazabar (Gaidam, Yunusari da Bursari) sun ce tun da wakilin nasu, ya sa kafa ya tafi Abuja a matsayin wakilinsu, bai sake waiwaiyar su ba da nufin gudanar musu wani aiki na raya kasa.
Jagoran kudurin kiranyen ga dan majalisar, Malam Babagana Aisami Geidam ya ce: “Muna sanar da ɗaukacin al’ummar Geidam, Yunusari da Bursari (Ngazargamu) cewa, a matsayinmu na al’ummar wannan yanki, mun fara yunkurin yi wa dan majalisarmu na tarayya ƙiranye, bisa rashin kyakkyawan jagoranci da rashin gabatar da ƙudurori kan abin da yake ci wa al’ummar wannan yanki tuwo a ƙwarya a wannan yankin.
- Mutane na komawa gida bayan janyejwar ambaliyar Maiduguri
- Mutane miliyan 1 ambaliya ta shafa —Zulum
- ’Yan takarar ciyaman 20 a Kano ’yan ƙwaya ne —NDLEA
“Tafiya ta yi nisa wajen wannan shiri, muna aiki tuƙuru babu dare babu rana domin tabbatar da wannan aikin don samarwa al’umma mafita.”
Ya kara da cewar, “Wannnan yankin na Ngazargamu ya sha fama da rikici na rashin zaman lafiya, wanda ya haifar da koma baya ta fuskar ilimi, tattalin arziƙi, noma da sauran fannonin rayuwa da dama.
“Amma wannan dan majalisar ya kasa taɓuka komai na kawo sauyi ga rayuwar al’umma da yake wakilta.
“Hakan ya sa muka yi wannan yunƙuri don yi masa ƙiranye wala-Allah zai dawo cikin taitayinsa,” in ji Babagana.
“Bisa tuntuɓa da muka yi, kusan kaso tamanin cikin ɗari (80%) na al’ummar wannan yankin ba su gamsu da wakilcin wannan dan majalisar ba.
“Duk inda ka samu mutum goma a zaune, idan ka tattauna da su to kuwa za ka tarar da takwas daga cikinsu suna nuna rashin gamsuwarsu ga jagorancin wannan dan majalisa namu.
“A matsayinmu na al’ummar Geidam, Yunusari da Bursari, har yanzu ba mu isa mu nuna ’ya’yan talakawa 12 da ya taimaka wa da wani abu na jari ko na abubuwan koyon sana’a ba.
“Hakazalika ba za mu i’a nuna mutum 12 wadanda ya yi wa sanadiyar aikin yi a gwamnatin tarayya kamar dan sanda, soja, Sibil Difens immigreshan da sauransu ba.”
A cewarsa, a shekarar 2019 ana cikin ɓarin wuta sakamakon harin ’yan Boko Haram, al’umma muka saida rayukanmu muka fito kwai da kwarkwata muka zaɓe shi, amma duk wani lokacin da iftila’i yake faruwa baya zuwa, babu ruwansa da al’ummar mazabarsa, babu aikin cigaba, babu ziyarar al’umma, babu kyakkyawan mu’amala tsakaninsa da al’ummar mazabarsa.
“Wannan dalilin ya sa a matsayinmu na al’ummar wadannan yanki, za mu yi amfani da damar da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba mu wajen yi wa ɗan majalisa ƙiranye domin dawo da shi gida idan bai taɓuka komai ba,” in ji Babagana.
Aminiya ta yi kokarinta don jin ta bakin wannan dan majalisar wakilai, Honarabul Lawan Shettima Ali, kan wannan batu, amma wayar sa ba ta shiga.
Wakilinmu ya tura masa sako ta wayarsa, amma har kammala wannan labari ba bu amsa daga gare shi.
“Sai dai kuma Aminiya ta tattauna da Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na yankin, Alhaji Kafci Geidam wannan dan majalisar ya fito ciki a kan ko wadannan mutane da suke kokarin kiranye.
Alhaji Kafci ya amsa da cewar lalle sun san da wannan yunkuri na wadannan mutane.
Amma a cewarsa, su wadannan mutane ba ’yan APC ba ne, a saninsa ’yan jama’iyyun adawa ne, wannan ita ce magana ta gaskiya.“